Bayan ceton rayukan giwaye a Bauchi, UK ta gwangwaje 'Dan Najeriya da kyautar N16m

Bayan ceton rayukan giwaye a Bauchi, UK ta gwangwaje 'Dan Najeriya da kyautar N16m

  • Wani dan Najeriya mai kula da namun daji ya samu lambar yabo kan kokarinsa wurin ceto rayukan wasu giwaye a jihar Bauchi
  • Mai kula da namun dajin mai suna Suleiman Seidu, ya samu lambar yabon 2021 Tusk Wildlife Ranger kan kokarinsa
  • Suleiman ya na aiki da Nigerian National Park Service da ke Yankari a jihar Bauchi inda ya ke kula da rayukan namun daji tun 1999

Wani dan Najeriya mai suna Suleiman Seidu ya samu lambar yabon Tusk Conservation kan gudumawar da ya bayar wurin kare rayukan namun dajin da za su iya karewa a Najeriya.

An bai wa mutumin lambar yabo kan kokarinsa da sadaukarwarsa wurin aiki tare da ceton rayukan giwaye a jihar Bauchi.

Na tsawon shekaru, Suleiman ya ki sakin aikinsa kuma ya sadaukar da rayuwarsa wurin ceton namun daji, The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hatsarin kwale-kwale: Fasto da wasu mutane shida sun mutu a jajiberin sabuwar shekara

Bayan ceton rayukan giwaye a Bauchi, UK ta gwangwaje 'Dan Najeriya da kyautar N16m
Bayan ceton rayukan giwaye a Bauchi, UK ta gwangwaje 'Dan Najeriya da kyautar N16m. Hoto daga Tuska Award
Asali: UGC

The Guardian Nigeria ta ruwaito cewa, an dauka Suleiman Seidu aiki a Nigerian National Park Service a shekarar 1999 kuma an tura shi Yankari Game Reserve da ke Bauchi inda ya dinga yaki da masu farauta tare da bai wa giwaye kariya.

Lambar yabon da ya samu ta kudi ce kuma ta kai Naira miliyan 16. Masu kula da lambar yabon Tusk Conservation sun sanar a shafinsu na yanar gizo cewa Suleiman mutum ne jajirtacce.

"Jajircewarsa, aikinsa tukuru, mayar da hankali da kuma gaskiyarsa ne ya sa abokan aikinsa da mutanen yankin ke sha'awarsa tare da ganin girmansa."

Ina sha'awar bai wa namun daji kariya, cewar Suleiman Seidu

A bangarensa, Suleiman ya ce ya na matukar kaunar namun daji kuma ya daukar wa kansa alkawarin bai wa wadanda za su iya karewa nan babu dadewa kariya.

Kara karanta wannan

An kuma: Ministan Buhari ya kama da annobar Korona bayan wasan buya da cutar

Ya ce babban burinsa shi ne bai wa namun dajin da za su iya karewa kariya saboda 'yan bayan sun amfana.

Hotunan tsoho mai shekaru 88 ya kammala digiri rana daya da jikarsa mai shekaru 23

A wani labari na daban, ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare. Wani tsoho mai shekaru 88 ya tabbatar da wannan karin maganar bayan cika burinsa wanda ya dauki tsawon lokaci a zuciyarsa.

Ya samu nasarar kammala digirinsa a jami’ar Texas da ke San Antonio inda ya yi karatu a fannin tattali.

Abinda zai kara burge mai karatu akan labarinsa shi ne yadda ya kammala digirin tare da jikarsa, Melanie Salazar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel