Abdullahi Abubakar
5769 articles published since 28 Afi 2023
5769 articles published since 28 Afi 2023
Kungiyar ƙabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo ta musanta jita-jitar cewa ta na shirin zuwa Sokoto domin ba 'yan Arewa hakuri kan juyin mulkin 1966 a Najeriya.
Tsohon karamin Ministan ilimi a Najeriya, Cif Kenneth Gbagi ya riga mu gidan gaskiya, marigayin ya rasu ne a jiya Asabar 4 ga watan Mayu a jihar Delta.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan ba 'yan sandan jihohi manyan makamai domin dakile wasu matsaloli.
Hadimin Gwamna, Babagana Umara Zulum a bangaren harkokin al'umma, Cif Kester Ogualili a ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya a yau Asabar.
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya sha alwashin sanya hannu a dokar kisan kai ga masu ba 'yan bindiga bayanan sirri wanda suke cutar da al'umma.
Tsohon mai neman shugabancin jam'iyyar APC, Mohammed Saidu-Etsu ya koka kan yadda aka naɗa Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar a Najeriya.
Babbar kotun jihar Anambra ta yankewa tsohon manajan bankin FCMB daurin shekaru 121 a gidan kaso bayan sace N121m na wani kwastoma daga bankin Microfinance.
'Yan bindiga sun yi ajalin mutane 24 wadanda mafi yawansu 'yan banga ne a karamar hukumar Sabuwa da ke jihar Katsina a daren ranar Alhamis 2 ga watan Mayu.
Hukumar EFCC ta na zargin akalla tsofaffin gwamnoni 54 a Najeriya da badakalar N2.187trn yayin da suke mulkin jihohinsu daban-daban tun bayan dawowar dimukradiyya.
Abdullahi Abubakar
Samu kari