Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Makarantar Horas Da Fastoci a Kaduna, Sun Sace Dalibai Da Dama

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Makarantar Horas Da Fastoci a Kaduna, Sun Sace Dalibai Da Dama

Kaduna - 'Yan Bindiga sun kai hari makarantar St. Albert the Great Institute of Philosophy, da cocin Kotolika ke kula da shi a garin Fayit a masarautar Kagoma da ke karamar hukumar Jama'a da ke Kaduna.

A cewar NewsWireNGR, 'yan bindigan sun kai harin ne a daren ranar Litinin.

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Makarantar Horas Da Fastoci a Kaduna, Sun Sace Dalibai Da Dama
Daliban Makarantar Falsafa ta St. Albert da ka Kaduna. Hoto: NewsWireNGR
Source: Facebook

Bata garin sun afka makarantar misalin karfe 8 na dare suka fara harbe-harbe, hakan ya janyo tashin hankali a yankin.

Wata majiya da ke zaune kusa da makarantar ta bayyana cewa 'yan bindigan sun shafe kimanin awa guda kafin mafarauta da 'yan sa-kai suka kawo dauki suka fatattake su.

Read also

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun saki wadanda aka tsare sun kona motocin sintiri

An kuma gano cewa 'yan ta'addan sun sace wasu daliban yayin da suka raunata wasu yayin harin.

Ba a tabbatar da adadin daliban da aka sace ba a lokacin hada wannan rahoton domin an yi kokarin ji ta bakin mahukunta makarantar amma hakan bai yi wu ba.

Ku saurari karin bayani ...

Source: Legit.ng

Online view pixel