Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare

Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare

  • Gwamna Babagana na jihar Borno ya ziyarci kasuwar dare ta garin Banki inda ya ci kasuwa tare da mazauna yankin
  • A daren Alhamis, gwamnan ya zagaya kasuwar wurin karfe 10:30 na dare inda ya dinga nuna farin cikinsa ga 'yan kasuwa
  • Garin Banki an san shi da zama cibiyar kasuwanci wacce ke da kasuwannin dare da na rana a iyakar Kamaru da Nijar

Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya ziyarci garin Banki a ranar Alhamis, gari da ya ke kusa da iyakar Najeriya da Kamaru, inda suka ci kasuwar dare bayan shekaru bakwai da rufe ta saboda ta'addanci.

Daily Trust ta ruwaito cewa, tare da rakiyar wasu jami'an gwamnati, Zulum ya ziyarci wasu manyan shaguna wurin karfe goma da rabi na dare.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan sa-kai sun kashe Limami da wasu mutane 10 a Sokoto

Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare
Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An gano cewa ya je tare da duba yadda garin ke habaka da al'amuran rayuwa da na tattalin arziki, hakan yasa ya kwatanta abinda ya gani da lokaci mafi farin ciki a rayuwarsa tun bayan hawansa gwamna.

Banki ya na daya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci da ke wajen Maiduguri. Garin na nan a karamar hukumar Bama kuma an san shi da kasuwannin dare da rana.

Komai ya tsaya cak ne sakamakon hauhawar ta'addanci a 2014, lamarin da ya tirsasa mazauna yankin tserewa zuwa Kamaru da jamhuriyar Nijar.

Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare
Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A yayin jawabi ga wasu 'yan sari a kasuwar a daren Alhamis, gwamnan ya ce:

"Alhamdulillah! Abun farin ciki ne yadda al'amuran kasuwanci suka dawo garin Banki. Duba Banki a karfe goma da rabi na yau.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Moghalu ya fice daga jam'iyyar YPP ya koma sabuwar jam'iyya

"Irin wannan cigaban na ke ta son ganin tuntuni. Ina tunanin yau ce rana mafi farin ciki a rayuwa ta saboda a yau ga ni cikin garin Banki a wannan lokacin.
"Na matukar gamsuwa saboda yanzu ba karfe goma na safe ba ne, karfe goma da rabi ce ta dare. Ina da tabbacin cewa duk mai son mu zai yi farin ciki kan wannan cigaban," Zulum yace.
Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare
Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ta'addanci: Gwamnonin yankin tafkin Chadi takwas sun gana a Kamaru

A wani labari na daban, Gwamnoni takwas na yankin tafkin Chadi sun gana a birnin Yaounde da ke jamhuriyar Kamaru a ranar Litinin inda suka tattauna kan matsalar tsaro da kuma hadin kan yankin, Daily Trust ta wallafa.

Taron da hukumar kula da tafkin Chadi, tare da hadin guiwar African Union, shirin cigaban majalisar dinkin duniya suka hada, gwamnatin Kamaru tare da hadin guiwar kungiyar gwamnonin tafkin Chadi suka bada masauki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar

Gwamnoni shida da suka hada da Babagana Umara Zulum na jihar Borno, Issa Lamine na Diffa daga Nijar, Midjiyawa Bakari na arewacin Kamaru, Abate Edii Jean na yankin arewacin Kamaru, Mahamat Fadoul Mackaye na yankin Lac da ke Chadi da Amina Kodjyana Agnes Hadjer ta Chadi duk sun halarci taron yayin da gwamnonin jihohin Adamawa da Yobe suka tura wakilai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel