Yanzu-Yanzu: Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar

Yanzu-Yanzu: Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar

  • Rahoto ya bayyana cewa, PDP ta amince a mika shugabancinta ga wani dan Arewacin Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan da jam'iyyar ta yi zaman zatarwa a yau Alhamis a Abuja
  • Batutuwa da dama sun shiga cikin tattaunawar inji rahotanni da muke samu daga majiyoyi

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar PDP a ranar Alhamis 7 ga watan Oktoba ya amince da karkatar da matsayin shugaban jam’iyyar zuwa Arewa.

Hukuncin ya biyo bayan amincewa da shawarwarin da ke kunshe cikin rahoton kwamitin karba-karba na babban taron jam’iyyar PDP na kasa wanda gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi ke jagoranta.

Yanzu-Yanzu: Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar
Manyan jam'iyyar PDP sun tattauna kan batutuwa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kwamitin karba-karba na Ugwuanyi ya musanya shugabanci da duk wasu mukamai na zababbun jam’iyyun da mutanen Arewa ke rike da su yanzu da na Kudu.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na ki amincewa da bukatar gwamnoni na dakatar da takarar Obasanjo a karo na biyu, Atiku

Kakakin PDP, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan taron na NEC.

Ya ce an umarci shugabannin jam’iyya a shiyyoyin siyasa shida da su koma sashi da kuma kananan bangarori daban-daban a zababbun mukamai tsakanin jihohi a jihohinsu daban-daban. .

Bisa ga dukkan alamu, biyo bayan takaddamar da ta tarbi musanyawar yankin, Ologbondiyan ya ce NEC za ta sake ganawa a wani lokaci don duba rahoton wani kwamiti da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ke jagoranta.

Kwamitin Bala Mohammed ya ba da shawarar cewa a ba da tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023 ga duk masu bukata, ba tare da la’akari da asalin kabilar su ba.

Ologbondiyan, duk da haka, ba bayyana manufar taron NEC na nufin tattaunawa kan rahoton Bala Mohammed zai gudana ba kafin babban taron jam'iyyar na 30-31 ga Oktoba.

Kara karanta wannan

An fara taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar PDP a Abuja

Taron na NEC ya samu halartar gwamnonin jam’iyyar, ‘yan majalisar kasa, tsoffin gwamnoni, tsoffin ministocin gwamnati da tsoffin shugabannin jam’iyyar.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar; shugaban kwamitin amintattu (BoT), Sanata Walid Jibrin; tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark da sauransu.

An fara taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar PDP a Abuja

A wani labarin, Babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya, Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 7 ga watan Oktoba, ta fara taron gaggawa na kwamitin zartarwar jam'iyyar na kasa (NEC) karo na 94.

Taron wanda ke wakana a Abuja yana gudana ne a zauren NEC, hedikwatar PDP ta kasa, Wadata Plaza a Abuja.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar na kasa, Umaru Tsauri, kuma Legit.ng ta gani, PDP ta umarci dukkan mambobinta da su shiga taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel