Ta'addanci: Gwamnonin yankin tafkin Chadi takwas sun gana a Kamaru

Ta'addanci: Gwamnonin yankin tafkin Chadi takwas sun gana a Kamaru

  • Gwamnoni takwas na yankin tafkin Chadi sun gana a jamhuriyar Kamaru a ranar Litinin da ta gabata
  • Gwamnonin da suka hada da Zulum, Gwamnonin Nijar da na Kamaru sun tattauna kan yadda za su kawo karshen rashin tsaro a yankin
  • Har ila yau, taron ya duba yadda za a kaddamar da sabbin tsarikan kawo daidaito tsakanin jihohin yankin wadanda aka tsara tun 2019

Yaounde, Kamaru - Gwamnoni takwas na yankin tafkin Chadi sun gana a birnin Yaounde da ke jamhuriyar Kamaru a ranar Litinin inda suka tattauna kan matsalar tsaro da kuma hadin kan yankin, Daily Trust ta wallafa.

Taron da hukumar kula da tafkin Chadi, tare da hadin guiwar African Union, shirin cigaban majalisar dinkin duniya suka hada, gwamnatin Kamaru tare da hadin guiwar kungiyar gwamnonin tafkin Chadi suka bada masauki.

Read also

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

Ta'addanci: Gwamnonin yankin tafkin Chadi takwas za su gana a Kamaru
Ta'addanci: Gwamnonin yankin tafkin Chadi takwas za su gana a Kamaru. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Gwamnoni shida da suka hada da Babagana Umara Zulum na jihar Borno, Issa Lamine na Diffa daga Nijar, Midjiyawa Bakari na arewacin Kamaru, Abate Edii Jean na yankin arewacin Kamaru, Mahamat Fadoul Mackaye na yankin Lac da ke Chadi da Amina Kodjyana Agnes Hadjer ta Chadi duk sun halarci taron yayin da gwamnonin jihohin Adamawa da Yobe suka tura wakilai.

A wata takarda da mai bai wa Zulum shawara, Malam Isa Gusau ya fitar, ya ce taron da firayim ministan Kamaru, Joseph Dion Ngute, wanda ya samu rakiyar Sarkin Yaounde, Luc Messi Atangama, an tattauna al'amuran tsaro wanda za su mayar da hankali kan dakile farmakin 'yan ta'adda tare da taimakon masu bukata.

Taron ya kara da duba yadda za a kaddamar da sabbin tsarikan kawo daidaito a yankin wanda aka shirya tun 2019, yayin da aka yi makamancin taron a Niamey, jamhuriyar Nijar.

Read also

Burtaniya ta aiko sojojin ruwanta zuwa Najeriya don magance matsalar tsaro

Kamar yadda takardar tace, Zulum a gudumawarsa, ya yi kira kan bukatar habaka hadin kai na tsakanin kasashen kan tsarin kafin a fara aiki da sabbin tsarikan.

"Duk wadannan shirin ba za su yuwu ba,ba tare da tsaro ba, abu na farko da muke bukata a dukkan yankin shi ne shawo kan matsalar tsaro ballantana a wuraren tafkin Chadi."
"Ya zama dole mu dauka babban mataki tare da tabbatar da tsaro a tafkin Chadi domin kawar da ta'addanci, idan ba haka ba, babu inda za su kai," Zulum yace.

Gwamnan ya bayyana damuwarsa kan yadda ba a amfani da tafkin Chadin wurin samar da tattalin arziki mai yawa a yankin.

Gwamnan Bornon ya ce ya na kokarin ganin ya samar da cibiyoyin kasuwanci a garin Banki da ke karamar hukumar Bama, Gamboru a Ngala, Baga a Kukawa da Damasak a karamar hukumar Mobbar domin inganta al'amuran tattalin arziki a yankin tafkin Chadin.

Read also

Majalisa ta tabbatar da nadin wanda ya fara karatu tun ba a haife shi ba a cikin mashawartan EFCC

Ta fashe: Sirrin kazamar dukiyar shugabannin duniya 35, 'yan siyasa 330 da biloniyoyi 130 a kasashe 91

A wani labari na daban, miliyoyin takardu sun bayyana kuma gagarumin binciken hadin guiwa na 'yan jarida ya bankado sirrikan dukiyoyin tsoffi da wasu shugabanni a duniya, 'yan siyasa da jami'an gwamnati sama da 330 a kasashe 91 na duniya.

Takardun sirrin sun bayyana wasu harkallar bakin teku na Sarkin Jordan, shugabannin kasashen Ukraine, Kenya da Ecuador, firayim ministan jamhuriyar Czech da tsohon firayim ministan Tony Blair.

Takardun sun bayyana yanayin hada-hadar kudin Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin da sama da biloniyoyin duniya 130 na kasashen Rasha, Amurka, Turkiyya da sauran kasashe, Premium Times ta wallafa.

Source: Legit

Online view pixel