Zamfara: Ƴan bindiga sun kashe mutum 19, ciki har da ƙananun yara, sun ƙone shaguna da gidaje

Zamfara: Ƴan bindiga sun kashe mutum 19, ciki har da ƙananun yara, sun ƙone shaguna da gidaje

  • Akalla mutane 19 ne su ka rasa rayukan su bayan ‘yan bindiga sun afka kauyen Kuryar Madaro dake jihar Zamfara
  • Lamarin ya auku ne a ranar Talata, cikin wadanda su ka halaka har da kananun yara sannan su ka banka wa shaguna wuta
  • Hakan ya auku ne washegarin da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkana ya kai wa ‘yan sandan dake hanyar Shinkafi zuwa Kaura Namoda ziyara

Zamfara - Yan bindiga sun halaka mutane 19 ciki har da yara sannan sun kona gidaje da shagunan mazauna kauyen Kuryar Madaro da ke jihar Zamfara a daren Talata.

Premium times ta ruwaito yadda su ka kai farmakin washegarin da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkana, ya kai wa ‘yan sandan musamman da suke aiki wuraren hanyar Shinkafi zuwa Kaura Namoda ziyara.

Read also

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

Zamfara: Ƴan bindiga sun kashe mutum 19, ciki har da ƙananun yara, sun ƙone shaguna da gidaje
'Yan bindiga sun kashe mutum 19, sun ƙone shaguna da gidaje. Hoto: Premium Times
Source: Facebook

Kauyen Kuryar Madaro a karkashin karamar hukumar Kaura Namoda yake amma ya na da iyaka da Zurmi da Shinkafi, wurin da ta’addanci ya fi yawaita a fadin jihar.

Wata majiya ta ce sun kwashe sa’o’i da dama su na ta’addanci a daren

Premium Times ta ruwaito yadda wata majiya ta sanar da BBC Hausa cewa ‘yan bindigan sun kwashe sa’o’i da dama a kauyen su na ta’addanci.

Sai da su ka saci abubuwa da dama a shaguna sannan su ka sace dabbobin da ake kiwo a gidaje.

Wata majiya ta daban, Mustapha Mai Leda ya tabbatar wa da Premium Times aukuwar farmakin.

Kamar yadda ya ce:

“Mun birne mutane 19 da ‘yan bindiga su ka halaka. Akwai mutane da dama da su ka raunana wadanda suke asibiti. Cikin wadanda su ka halaka har da kananun yara da mata wadanda su ka kasa tserewa yayin da su ka kai farmakin.”

Read also

Katsina: ‘Yan sanda sun kama tsohuwar ma’aikaciyar hukumar NIS bisa damfara ta N47m

Wata majiyar ta daban ta ce ‘yan bindigan sun banka wa gidaje 13 da ababen hawa 16 wuta, ciki har da na ‘yan sandan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Mohammed Shehu ya tabbatar da farmakin, sai dai bai fadada bayani a kai ba.

Yadda 'yan sandan Zamfara suka kama 'yan bindiga 69 da masu hada baki da su

A wani labarin daban, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana yadda ta samu nasarar kama mutane 21 da ake zargin ‘yan bindiga ne da su ka addabi jihar tare da masu taimaka musu guda 69 duk a cikin watan Satumba.

SP Muhammed Shehu, jami’in hulda da jama’an hukumar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau, inda yake lissafo tarin nasarorin da jami’an tsaro su ka samu a jihar.

Kamar yadda ya bayyana, sun halaka shu’uman ‘yan bindiga 5 da jami’an tsaro su ka bayyana su na nema ido rufe.

Read also

Dalilin da ya sa ƴan bindiga su ke kai farmaki wasu garuruwa 2 a Katsina, Ƴan Sanda

Source: Legit.ng

Online view pixel