Yobe: Mata mai juna biyu ta haɗa baki da wasu maza 2 wurin garkuwa da kanta

Yobe: Mata mai juna biyu ta haɗa baki da wasu maza 2 wurin garkuwa da kanta

  • Wata Nafisa Saleh ta hada kai da mutane 2 wurin garkuwa da kan ta
  • Lamarin ya faru ne a Damaturu, babban birnin jihar Yobe
  • Tun ranar 1 ga watan Oktoban 2021 ta boye yayin zuwa asibiti yin awo

Jihar Yobe -Wata mata mai suna Nafisa Saleh, mai ciki, ta hada kai da mutane 2 wurin garkuwa da kan ta a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, an neme ta an rasa ne tun ranar 1 ga watan Oktoban 2021 tana hanyar zuwa asibitin kwararru dake Damaturu don yin awo.

Yobe: Mata mai juna biyu ta haɗa baki da wasu maza 2 wurin garkuwa da kanta
Mata mai juna biyu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar BUK a Kano

Bayan garkuwa da ita, wadanda su ka hada kai da ita sun kira mijin ta inda su ka bukaci ya biya kudin fansa.

Ta yi hakan ne don tatsar kudi wurin mijin ta da ‘yan uwan ta

Saidai binciken ‘yan sanda ya bayyana cewa daga baya aka gano cewa Nafisa da kanta ta sa aka yi garkuwa da ita don tatsar kudi a hannun mijin ta da ‘yan uwan ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim a wata takarda ta ranar Talata ya bayyana cewa ‘yan sanda sun yi gaggawar fara aikin su sannan su ka gano gaskiyar lamarin.

A cewar sa, rundunar ‘yan sanda ta kama mutane 2, Goni Modu da Umar Mai Gudusu duk ‘yan kauyen Dadinge dake karamar hukumar Gujba a jihar.

Saidai an yi gaggawar wucewa da Nafisa zuwa asibiti don duba lafiyar ta saboda halin da aka tsince ta a ciki.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Dungus ya kara da bayyana cewa sun kama wasu mutane 2 da ake zargin sun yi garkuwa da wani yaro mai shekaru 3 a karamar hukumar Potiskum dake jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

Masu garkuwa da mutanen duk yara ne kanana

A cewar sa:

“Duk wadanda ake zargin yara ne, daya shekarun sa 14 dayan kuma 12, sai dai na ukun ya tsere.
“Idan ba a manta ba a ranar 18 ga watan Satumban 2021, an yi garkuwa da Adamu Abubakar Baban Yaro mai shekaru 3, sannan an sake shi bayan amsar N50,000 a matsayin kudin fansa.”

Ya kara bayyana yadda rundunar ta zage wurin bincike don kama duk wasu miyagun mutane a fadin jihar.

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kuɗin fansa

A wani labarin daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta samu nasarar damkar masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kudin fansar yaro dan shekara 7, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Litinin inda ya ce sun kama wani Muhammed Abubakar mai shekaru 42 da Clinton Niche mai shekaru 18.

Kara karanta wannan

Adamawa: Magidanci mai 'ya'ya 3 ya rasa ransa bayan shan guba da ya yi sakamakon rikici da matarsa

Oyeyemi ya ce mahaifin yaron, Stephen Ajibili, ya kai korafin satar dan sa, Daniel, da aka yi inda ya ce mahaifiyar sa tana tsaka da aiki da misalin karfe 11:20am aka sace shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel