Rashin tsaro: Yadda aka hallaka mutane kusan 700 a cikin kwanaki 30 a jihohin Najeriya

Rashin tsaro: Yadda aka hallaka mutane kusan 700 a cikin kwanaki 30 a jihohin Najeriya

  • WANEP tace mutum sama da 690 aka kashe a Najeriya a watan Agustan 2021
  • Kashe-kashen ya fi kamari a Filato, Zamfara, Kaduna, Katsina, Neja, da Borno
  • Sannan a cikin kwana 30, ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane kusan 500

Nigeria – Kungiyar WANEP tace a watan Agustan 2021, akalla mutane 693 suka rasa ransu a Najeriya a dalilin hare-haren da ake kai wa a jihohin kasar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto kungiyar WANEP da ke bincike a Afrika ta yamma tana cewa an rasa rayuka 183 wajen fada tsakanin jami’an tsaro da ‘yan ta’adda.

West Africa Network for Peace building tace an kashe mutane 129 a rikicin kungiyoyin asiri, ‘yan bindiga, zanga-zanga, kisan-kai, rikicin makiyaya da manoma.

Kara karanta wannan

Sojoji sun damke tsohon soja yana jigilar tulin wiwi da kwayoyi daga Ondo zuwa Jihohin Arewa

Har ila yau mutane akalla biyu sun mutu a sakamakon rikicin jinsi a watan Agustan da ya gabata.

An sace mutane kusan 500

Binciken da kungiyar West Africa Network for Peace building ta gudanar, ya nuna cewa an yi garkuwa da mutane sama da 490 a jihohi 18 a cikin wata daya.

Jamian tsaro
Sojojin Najeriya a Bama Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a Agustan, akwai mata 37, da kuma kananan yara 22.

Har ila yau wannan bincike ya nuna 97% na wadanda aka kashe, masu fararen hula ne; mata 23 da yara 17. Ragowar mutane 19 da aka kashe, jami’an tsaro ne.

Ya kashe-kashen suke a jihohi?

Rahoton yace jihar Filato ce aka samu ta zo ta farko da mutuwar mutane 122. A jihohin Oyo, Enugu, Kuros Riba, mutum dai-daya rak aka ji an kashe.

Kara karanta wannan

Yadda wani mutum ya dirka wa direban keke-napep duka nan take ya mutu

A jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina, Neja, da Borno, alkaluman sun nuna an rasa mutane 121, 111, 64, 37, da 27, a jihohin biyar an hallaka mutane har 360.

Mutum 26, 24, 21, 18, 15, 14, 13, 7, da kuma 7 suka mutu a jihohin Imo, Ribas, Ogun, Benuwai, Delta, Osun, Legas, Ondo da kuma Taraba a daidai wannan lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel