Yajijn aikin likitoci: Likitoci sun ce Osinbajo ne kadai zai iya magance matsalarsu

Yajijn aikin likitoci: Likitoci sun ce Osinbajo ne kadai zai iya magance matsalarsu

  • Kungiyar likitoci mazauna kasa sun bayyana cewa, sun yi imanin Osinbajo zai magance damuwarsu
  • Sun bayyana haka ne bayan ganawa da suka yi da mataimakin shugaban kasan jim kadan bayan nada shi wani mukami
  • Sun bayyana cewa, ba za su dage yajin aikin da suke ciki ba har sai sun samu tabbaci mai karfi daga Osinbajo

Abuja - Kungiyar likitoci mazauna kasa (NARD) ta amince da nadin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin shugaban kwamitin sake fasalin kiwon lafiya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar, a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba inda ta bayyana cewa shi kadai ne fatansu.

Dokta Okhuaihesuyi Uyilawa, shugaban NARD, ya fadi haka ne yayin da yake magana ashirin Channels TV na al'amuran yau da kullum, Sunrise Daily.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamnonin APC 5 da ka iya tsayawa takara a gefen Goodluck Jonathan

Yajijn aikin likitoci: Likitoci sun ce Osinbajo ne kadai zai iya magance matsalarsu
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Facebook

Uyilawa ya ce:

"Mataimakin shugaban kasa shine kawai fatan mu, mun hadu da shi a ranar Juma'a, kuma abin takaici, a ranar Asabar, muka samu alamar da ba daidai ba daga ministan kwadago, wannan na sirri ne. Ya yi kama da son kai a yanzu."

Wadannan batutuwa na zuwa ne bayan da kungiyar ta gana da mataimakin shugaban kasa Osinbajo ta manhajar Zoom, inda kungiyar ta ce Osinbajo ne ya nemi su yi ganawar.

Da aka tambaye shi ko kungiyarsa ta yi imanin mataimakin shugaban kasa na da mutunci a idon kungiyar, shugaban NARD ya ce:

"Yana da mutunci, amana, kuma shi ne wanda na yi imani zai iya sa abubuwa su yi aiki."

A nasa bangaren, mataimakin shugaban NARD, Adejo Arome, wanda ke tabbatar da ganawar Osinbajo da hukumar, ya shaidawa manema labarai ciki har da Legit.ng cewa sun gana ne ta hanyar amfani da manhajar Zoom a ranar Juma’a, 3 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Arome ya ce mataimakin shugaban kasar ya nemi bayanai na farko kan abubuwan da ke faruwa.

A cewar Arome:

“Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya tuntube mu. Ya gana da shugaban jiya (Juma'a). Hakika ganawar ta Zoom ya yi da shugabanmu duk da cewa wasu daga cikin mu na can. Shi (Osinbajo) ne ya bukaci ganawar domin yana son samun bayanin abin da ke faruwa.
"Ya ce yana bukatar cikakkun bayanai na duk abin da ya faru. Ya yi tambaya cikin natsuwa kuma mun yi imani zai yi wani abu kuma mun yi imani cewa nan ba da jimawa ba, zai kira mu a hukumance.
"Mun ba shi bayanin. Bayanan da muka ba shi na farko ne kuma ingantattu. Muna da tabbacin cewa sauran jami’an gwamnati ba za su ba shi dukkan cikakkun bayanai game da batun baki daya ba.
“Ya gaya mana cewa baya son a warware batun yanzu kuma daga baya a sake wani yajin aiki.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun roki Buhari ya mika kujerarsa zuwa kudancin Najeriya a zaben 2023

"Ya ce yana son ya kawo karshen matsalar lokaci daya. Muna jiran ya gayyace mu a hukumance kuma mun tabbata cewa zai yi. Mun amince da hukuncinsa."

Ba zamu dakatar da yajin aiki ba sai mun ji ta bakin Osinbajo

A bangare guda, Kungiyar ta sha alwashin cewa ba za ta dakatar da yajin aikin sama da wata daya ba ba tare da sa hannun mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo ba.

Osakhuesuyi Uyilawa, ya ce kungiyar za ta kira komawa bakin aiki ne kawai idan ta samu tabbaci daga Farfesa Osibanjo, Daily Sun ta ruwaito.

Rahoto: Jerin manyan jihohi 10 da suka fi yawan kwararrun likitoci a Najeriya

A bangare guda kuma, ministan ya dage kan cewa Najeriya na da isassun likitocin da za su kula da mutane, yana mai cewa matsalar likitocin ita ce ba a turawa da rarraba ma'aikatan kiwon lafiya daidai gwargwado a wuraren da suka dace.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hallaka dan Sanata Bala Na'Allah da aka yi

Ya ce yawancin likitocin kasar nan basu son aiki a yankunan karkara, sun zabi yin aikinsu a birane irinsu Abuja, Legas da Fatakwal.

Baya ga kwararrun likitocin cikin gida, Ngige ya ce likitocin da aka horar daga kasashen waje suma suna dawowa Najeriya don yin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel