Rikicin Jos: El-Rufa'i ya yi alkawarin magance matsalar tsaro a Jos da Kaduna

Rikicin Jos: El-Rufa'i ya yi alkawarin magance matsalar tsaro a Jos da Kaduna

  • Gwamnan jihar Kaduna ya yi alkawarin hada kai da na jihar Filato don magance matsalolin tsaro
  • Ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarar jajantawa a jihar ta Filato biyo bayan kashe-kashe da suka faru
  • Gwamnan ya ce, jihar Kaduna da ta Filato jihohi ne masu kamanceceniya ta fuskoki da yawa

Plateau - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da takwaransa na jihar Filato, Simon Bako Lalong, sun yi alkawarin hada kai da rundunar Operation Safe Haven (OPSH) da sauran hukumomin tsaro don magance matsalolin tsaro da ke addabar jihohin biyu.

Sun yi wannan alkawari ne ranar Lahadi 5 ga watan Satumba lokacin da El-Rufai ya ziyarci Lalong don jajantawa gwamnati da mutanen jihar Filato kan hare-hare da kashe-kashen da aka yi a wasu sassan jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

Rikicin Jos: El-Rufa'i ya yi alkawarin magance matsalar tsaro a Jos da Kaduna
Malam Nasiru El-Rufai | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamna El-Rufai ya ce:

“Filato da Kaduna ba makwabta ne kawai ba. Muna da dangantaka mai karfi kuma tun lokacin da muka hau mulki a 2015, ni da Gwamna Lalong muna tuntubar juna; Gwamna Lalong ne ya gabatar da mu ga Cibiyar Tattaunawar Ba da Agaji, wata kungiya mai zaman kanta ta duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya.
“Gwamna Lalong ne ya gabatar da ra’ayin cewa ya kamata jihohin biyu su kafa hukumomin gina wanzar da zaman lafiya.
"Filato tana da Hukumar Wanzar da Zaman Lafiya kuma Kaduna tana da Kwamitin Zaman Lafiya, muna aiki tare domin mun fahimci cewa jihohin mu biyu suna da girma kuma gidaje ne ga mutane da yawa a fadin Najeriya.
“Har sai idan mun inganta zaman lafiya tsakanin mutane daban-daban, sabanin haka rikici ba zai shafi jihohin biyu kadai ba har ma da kasar baki daya. Dangane da rikicin baya-bayan nan tsakanin Irigwe da Fulani, muna da Irigwe a Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Kada ku bankawa Najeriya wuta da kalaman kiyayya, FG ta gargadi shugabanni

"Muna kuma da Ganawuri da Atakar a sassan Kudancin Jihar Kaduna, mu mutane daya ne kuma dole ne mu hada kai mu hada kan mutanen mu don mu zauna lafiya".

Lalong, wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, Farfesa Sonni Tyoden, ya ce hada kai tsakanin jihohin biyu zai dakile barazanar tsaro da ke fuskantar su.

Lalong ya jinjina wa El-Rufa’i bisa zuwansa don jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Filato kan rikice-rikicen da ke faruwa a jihar.

A bayanansa:

“Gaskiya ne Filato da Kaduna ba makwabta ne kawai ba, alabashshi suna da tarihi na dogon lokaci, don haka abin da ya shafi Filato ya shafi Kaduna kuma abin da ya shafi Kaduna ya shafi Filato.
“A wannan lokacin bakin ciki, zai saukaka lamurra lokacin da abokai masu tunani iri daya suka zo don magance matsalarsu. Muna godiya da nuna kawancen ku, muna godiya da tausayawar ku."

Gwamnatin Kaduna ta haramta cin kasuwannin mako-mako a kananan hukumomi biyar

Kara karanta wannan

Akume ya roki EFCC ta yi ram da gwamnan Benue Ortom ta bincikeshi kan wasu kudi

Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatar cin kasuwan mako-mako da aka saba dashi a wasu sassan jihar bayan duba da nazirin tabarbarewar tsaro a wasu kananan hukumomin jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da lamurran tsaro suke kara ta'azzara a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, musamman a jihar Kaduna inda aka samu sabbin hare-hare da suka hada da farmakar Kwalejin sojoji a makon jiya.

Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da sabuwar sanarwar dokar ne dauke da sa hannun kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, wanda Legit.ng Hausa ta samo a yau Litinin 30 ga watan Agusta.

Wani yankin sanarwar na cewa:

"Bayan cikakken nazari kan yanayin tsaro da shawarwarin da hukumomin tsaro suka bayar, Gwamnatin Jihar Kaduna na fatan sanar da dakatar da cin dukkan kasuwannin mako-mako a kananan hukumomin Birnin Gwari, Igabi, Giwa, Chikun da Kajuru nan take."

Doka a Zamfara: Gwamna ya ba da umarnin a harbe masu goyon biyu a babur

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun fasa coci, sun yi awon gaba da masu ibada

Kamar dai a jihar ta Kaduna, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ba da umarnin rufe dukkan kasuwannin mako-mako a jihar a matsayin wani mataki na magance matsalar tabarbarewar tsaro a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa gwamna Matawalle ya sanar da hakan ne bayan ya karbi dalibai 18 da aka yi garkuwa da su a Kwalejin Aikin Gona da Kimiyyar Dabbobi ta Jihar dake garin Bakura.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatin jihar ta hana sayar da man fetur a cikin jarkoki a wani mataki na dakile samar da man ga 'yan bindiga, hakazalika da kuma ba da umarnin harbin masu babur dake goyon biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel