Kada ku bankawa Najeriya wuta da kalaman kiyayya, FG ta gargadi shugabanni

Kada ku bankawa Najeriya wuta da kalaman kiyayya, FG ta gargadi shugabanni

  • Gwamnatin Najeriya roki shugabanni da cewa, ya kamata su zama masu wanzar da zaman lafiya
  • Wannan na fitowa ne daga bakin ministan yada labarai da al'adu a Najeriya, Alhaji Lai Mohammed
  • Lai Mohammed ya lura cewa, a kasar an samu shugabannin da ke watsa kalaman kiyayya da tunzura mabiyansu

Cape Verde - Gwamnatin tarayya ta gargadi shugabannin siyasa da na addini da su daina “fitar da kalaman kiyayya” da za su iya cinnawa kasar wuta, TheCable ta ruwaito.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, neya yi wannan gargadi yayin da yake zantawa da NAN a ranar Laraba 1 ga watan Satumba a tsibirin Sal, Cape Verde.

A cewar kamfanin dillancin labarai na NAN, ministan ya je Cape Verde ne don halartar taro karo na 64 na hukumar kula da yawon bude ido ta Majalisar Dinkin Duniya (UNWTO) a Afirka da kuma bugu na biyu na dandalin saka hannun jari na duniya na UNWTO.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya kori ministocinsa biyu

Kada ku bankawa Najeriya wuta da kalaman kiyayya, FG ta gargadi shugabanni
Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake magana a gefen taron na duniya, ministan ya kuma gargadi kafafen yada labarai, musamman gidajen watsa labarai, da su bi ka’idar watsa labarai da sauran ka’idojin da aka gindaya musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"A cikin 'yan makonnin da suka gabata, kasar ta kasance mai ban tsoro, musamman a kafofin watsa labarai, tare da maganganun da ke haifar da tashin hankali lamarin da ya haifar da fargaba a Najeriya."
“Kalaman kiyayya da ke fitowa daga bakin 'yan siyasa, shugabannin addini da wasu gungun masu ra’ayi na da karfin da za su iya cinna wa kasar wuta.

A cewar ministan, wasu kalaman na ingiza wata kabila kan wata ko kuma wani addinin kan wani.

Ya kara da cewa:

“Babban shawararmu ga masu ruwa da tsaki shi ne ya kamata su fahimta kuma su tuna cewa shugabanci yana da nauyi da yawa, su rage kalaman kiyayya saboda suna da illa ga kasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Gwamnati na iya kokarinta wajen inganta kasa

Ministan ya ce gwamnati na kokarin rage kalubalen tsaro a kasar, kuma abin da take bukata shi ne hadin kai da karfafawa daga masu ruwa da tsaki, kamar yadda yazo a jaridar The Nation.

A kalamansa cewa yayi:

"Mun yarda cewa akwai kalubale amma gwamnati na iya bakin kokarin ta wajen magance rashin tsaro, bindiganci, tayar da zaune tsaye da kuma daidaita tattalin arziki."
"Abin da ake tsammanin daga wadannan shugabannin a wannan lokacin jarrabawa shine hadin kai da karfafawa.

Ya koka kan yadda shugabanni kan yadda suke kalaman da ke rarraba kan kasa.

A bangare guda, Lai Mohammed ya kara da cewa:

“Wasu kalmomin da muke jin tsoron amfani da su a baya kamar kisan kare dangi da kuma karar da kabilu, yanzu sune ke yawo a kafafen watsa labarai.
"Wannan shine dalilin da ya sa yake da mahimmanci a kira kowa da kowa don yin kira ga tunanin kishin kasa da ya kamata su fahimci hakan saboda akwai kasar da ake kira Najeriya, shi yasa suka zama shugabanni.

Kara karanta wannan

Cikar Najeriya shekaru 61: FG ta kafa kwamitin mutum 12 domin shirye-shirye

"Idan abin da suke fata ya faru, ba za su zama shugabanni ba sai dai bayi a wasu kasashe."

Ya ce Hukumar Watsa Labarai ta Kasa (NBC) da sauran masu gudanar da aikin watsa labarai za su tabbatar da cewa gidajen watsa shirye-shirye suna bin dokokin doka da da’a.

Ya ce duk gidan rediyon da ya keta dokar watsa shirye-shirye da da’a za a “daga masa jan kati”.

'Yan APC sun roki Buhari ya mika kujerarsa zuwa kudancin Najeriya a zaben 2023

A wani labarin, wata kungiya a jam'iyyar APC mai suna South East Mandate (SEM), ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saukaka hanyoyin zabar dan takarar shugaban kasa daga amintattun mambobin jam’iyyar na Kudu maso Gabas a zaben 2023.

Ta ce manufarta ita ce tabbatar da an samu shugaba daga yankin na Kudu maso Gabas a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari, Daily Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kashe-Kashen Jos: CAN ta miƙa muhimman saƙo ga shugabannin musulmi da kirista a Plateau

Kungiyar ta bukaci jam’iyyun siyasa a Najeriya da su mika tikitin takarar shugaban kasar nan zuwa Kudu maso Gabas bisa adalci, gaskiya da lamiri mai kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel