Doka a Zamfara: Gwamna ya ba da umarnin a harbe masu goyon biyu a babur

Doka a Zamfara: Gwamna ya ba da umarnin a harbe masu goyon biyu a babur

  • Gwamnan jihar Zamfara ta dakatar da yawan zirga-zirga a jihar da kuma dakatar kasuwanni
  • An dakatar kasuwannin mako-mako a duk fadin jihar tare da hana sayar da man fetur a jarkoki
  • Gwamnati ta kuma gargadi 'yan jihar da su kasance masu bin umarnin doka, kuma za a hukunta masu saba doka

Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ba da umarnin rufe dukkan kasuwannin mako-mako a jihar a matsayin wani mataki na magance matsalar tabarbarewar tsaro a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa gwamna Matawalle ya sanar da hakan ne bayan ya karbi dalibai 18 da aka yi garkuwa da su a Kwalejin Aikin Gona da Kimiyyar Dabbobi ta Jihar dake garin Bakura.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatin jihar ta hana sayar da man fetur a cikin jarkoki a wani mataki na dakile samar da man ga 'yan bindiga, hakazalika da kuma ba da umarnin harbin masu babur dake goyon biyu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur, ta bayyana dalili

An dakatar da cin kasuwannin mako-mako a jihar Zamfara saboda harin 'yan bindiga
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle | Hoto: dailyrust.com.ng
Asali: Facebook

Ya fadi cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gidajen mai a cikin jihar kuma ya kamata su sayar da mai na N10,000 kacal ga kowane abin hawa kuma ya kamata su kasance masu lura da motoci ko babura masu zuwa don sake sayayya nan take.
“Ba a yarda masu babur na kabu-kabu su dauki mutum uku lokaci guda ba.
“Mun kuma rage ayyukan babur da a daidaita sahu na kasuwanci tsakanin karfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na dare a babban birnin jihar, yayin da a wajen babban birnin jihar kuma ke tsakanin karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
”Amma muhimman ayyuka da za a hada da; Ma’aikatan lafiya, jami’an tsaro da ‘yan jarida da suka bayyana kansa an ba su damar hawa babur ko a daidaita sahu fiye da lokacin da aka bayyana."

Gwamnan ya kuma hana zirga-zirgar shanu, da itacen makamashi a duk fadin jihar, yayin da dole ne a gudanar da bincike sosai kan kayan abinci don tabbatar da cewa bai kai ga 'yan bindiga ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An harbe mutum 11 har lahira a sabon harin da aka kai Katsina

Yayin da yake cewa dole ne dukkan 'yan jihar su bi sabbin umarnin ko kuma su fuskanci fushin doka, gwamnan ya kuma yi kira ga jama'a da su kai rahoton duk wani wanda aka samu yana saba umarnin.

A wani bangare na sabbin dokokin, gwamnan ya ba da umarnin harbe masu babur dake daukar fasinjoji biyu a wani yunkuri na dakile matsalar tsaro a yankin, Tribune Nigeria ta ruwaito.

'Yan bindiga sun sako daliban kwalejin noma da suka sace a jihar Zamfara

An sako malaman makaranta da daliban kwalejin aikin gona da kimiyyar dabbobi ta jihar Zamfara dake Bakura.

Wata majiya daga tushe na kusa da gwamnatin jihar Zamfara da ta nemi a sakaya sunanta ta sanar wa jaridar Punch cewa za a kawo su gidan gwamnati gobe Juma'a 27 ga watan Agusta, amma, ya ki yin karin bayani.

Idan za a iya tunawa a ranar 16 ga watan Agusta, 2021 wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai hari kwalejin tare da sace mutane 19 da suka hada da ma'aikata uku, dalibai 15 da direba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sako daliban kwalejin noma da suka sace a jihar Zamfara

Bayan shafe kwanaki 88, 'yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace

A wani labarin, Sama da dalibai 70 'yan bindiaga suka sako na makarantar Islamiyya da ke garin Tegina wadanda aka yi garkuwa da su kwanaki 88 da suka gabata, PR Nigeria ta ruwaito.

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, an sace daliban ne a harabar makarantar Islamiyyar dake Tegina a watan Yunin 2021.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar PRNigeria cewa daliban na kan hanyarsu ta zuwa Minna akan hanyar Kagara daga Birnin Gwari.

An tsare daliban Islamiyyar na tsawon kwanaki 88 da awanni 11 gwargwadon lokacin da suka shafe a hannun 'yan bindigan kenan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel