Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

  • Goyon bayan da Sanata Ali Modu-Sheriff ke samu gabanin babban taron APC na kasa na kara karfi a kowane mako
  • Tsohon gwamnan na jihar Borno ne zabin wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a fadin kasar
  • Daya daga cikin abokan siyasarsa a jiharsa ta Borno, Mustapha Gambo, ya ce Sheriff zai kai APC ga tafarkin ci gaba

FCT, Abuja - Wani jigo a jam'iyyar APC na jihar Borno, Mustapha Gambo, ya ce tsohon gwamnan jihar, Sanata Ali Modu-Sheriff yana da abin da ake bukata domin sabonta APC idan ya zama shugaban jam'iyyar na kasa.

Gambo, wanda ya kasance mataimaki ga tsohon gwamnan jihar Borno, Ibrahim Shettima, ya fadi hakan ne a wata hira da yayi da jaridar The Punch a Abuja, a ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Buni ya yi martani kan korarsa da aka yi a matsayin shugaban APC, ya ce umurnin Kotu ba a kansa bane

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki
Jigon APC ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki Hoto: Yobe state government
Asali: Facebook

Ya ce takardun shaidar zama dan kasuwa da dan siyasa mai zurfin tunani ya sa ya cancanci hawa matsayin babban mukami.

Ya ce:

“Jam’iyyar APC tana bukatar karfi tare da girmamawa ga duk wadanda ke da burin yin takarar kujerar shugaban jam’iyyar mu, babu ko daya daga cikinsu da ke da abin da Mai girma Sanata Ali Modu Sheriff ya kawo.
"Zuwa yanzu Sheriff shi kaɗai ne ke zagaye a cikin ƙasar, yana shiga tsakanin membobi da shugabannin jam'iyyar a matakin ƙasa domin shirye -shiryen babban taron ƙaramar hukumar da za a yi a karshen wannan makon a ƙasa baki ɗaya."

Shugaban APC da aka kora ya magantu kan sallamarsa daga jam'iyyar, yayi magana akan komawa PDP

Sulaiman Adamu, shugaban jam’iyyar APC da aka kora a karamar hukumar Yola ta kudu, ya roki magoya bayansa da su ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron karamar hukuma

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Adamu a ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba ya bayyana korarsa daga APC a matsayin nufin Allah wanda yake karba da zuciya daya.

Legit.ng ta tattaro cewa Adamu, ya ce har yanzu jam'iyyar ba ta sanar da shi hukuncinta a hukumance ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel