Ku Dena Bamu Cin Hanci, Ƴan Sanda Da FRSC Sun Roƙi Ƴan Nigeria

Ku Dena Bamu Cin Hanci, Ƴan Sanda Da FRSC Sun Roƙi Ƴan Nigeria

  • Hukumomin yan sanda da FRSC a Nigeria sun gargadi mutane su dena bawa jami'ansu cin hanci kuma su yi karar duk wanda ya nemi su bashi
  • Yan sandan da FRSC sun yi wannan gargadin ne yayin wani taro kan yaki da rashawa da kwamitin shugaban kasa ta PACAC ta shirya
  • Hukumomin tsaron sun ce yan kasa na da muhimmin rawa da za su taka wurin kawo karshen cin hanci da rashawa

A wani mataki na kokarin kawar da rashawa, rundunar yan sandan Nigeria da ta jami'an hukumar kiyayye haddura, FRSC, sun karfafawa yan Nigeria gwiwa su dena bawa jami'ansu cin hanci, News Wire NGR ta ruwaito.

A cewar rahoton na News Wire NGR, hukumomin sun kuma shawarci mutane su rika kai karar duk wani jami'in da ya nemi karbar cin hanci daga hannunsu.

Ku Dena Bamu Cin Hanci, Ƴan Sanda Da FRSC Sun Roƙi Ƴan Nigeria
Jami'an Yan Sandan Nigeria. Hoto: News Wire NGR
Asali: Depositphotos

Hukumomin tsaron sun bada wannan shawarar ne yayin wani taron kwana daya da kwamitin shugaban kasa na yaki da rashawa, PACAC, ta shirya da aka yi ta hanyar amfani da fasahar intanet.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun yi ram da wasu maza biyar da ke lalata da junansu a Kano

Sakataren PACAC, Farfesa Sadiq Radda, ya ce yan kasa suna da muhimmin rawa da za su taka wurin kawo karshen rashawa da cin hanci. Ya yi imanin cewa za a takaita kananan rashawa idan mutane suna bin dokoki sannan hukumomi na ayyukansu yadda ya kamata.

Wane mataki ya dace ku dauka idan an nemi ku bada cin hanci?

Mataimakin kwamishinan yan sanda, Olaolu Adegbite, na sashin tattara binciken sirri, yayin jawabinsa a taron ya bukaci yan Nigeria su yi karar duk wani jami'i wurin tawagar X-Squad, tawagar sa ido ta IGP da sashin karbar korafin mutane, PCRU.

Ya ce:

"X-Squad na saka ido ne kan halayen da suka saba doka. Mutane suna iya kai korafi wurin su. Tawagar sa ido ta IG ita ma tana kai samame da kama jami'ai masu laifi. Ya kamata mutane su gabatar da hujja. Ya kamata su dena bada cin hanci, wanda hakan ma laifi ne."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke 'yan sa kai 7, sun bankawa motar yaki wuta

A jawabinsa, babban jami'in FRSC, Ntukidem Godwin, ya ce hukumar ta fara amfani da kyamara na jiki domin sa ido kan abin da jami'anta suke yi na Abuja, ya kara da cewa za a yi wa sauran jihohi hakan.

Ya ce:

"Kada ka saba dokar hanya ko tuki, kada ka bawa jami'an mu cin hanci. Kada ka ja hankalin mu da rashawa domin mu kyalle ka."

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

Kara karanta wannan

A kan N1000, Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Tsananin Duka a Adamawa

An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel