‘Yan sanda sun yi ram da wasu maza biyar da ke lalata da junansu a Kano

‘Yan sanda sun yi ram da wasu maza biyar da ke lalata da junansu a Kano

  • 'Yan sanda a Kano sun kama wasu maza biyar da suka yi lalata da wani matashi
  • Wadanda ake zargin dai sun yi amfani da sigar yaudara wajen jan yaron zuwa wurare daban-daban don yin luwadi da shi
  • Sai dai rundunar 'yan sandan ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kafin a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu

Rahotanni sun kawo cewa rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta damke wasu maza biyar da suka yi lalata da wani matashi.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa an cafke mutanen ne bayan da iyayen yaron suka kai korafi ofishin ‘yan sanda kan yadda mutanen suka dunga jan shi zuwa wurare mabanbanta suna luwadi da shi.

‘Yan sanda sun yi ram da wasu maza biyar da ke neman junansu da lalata a Kano
‘Yan sanda sun kama wasu 'yan luwadi a Kano Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Mai magana da yawun rundunar jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce bayan matashin mai shekara 20 ya yi ta fama da matsanancin ciwon ciki ne sai mahaifiyarsa ta nemi jin ainihin abin da ke damunsa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan sanda a Zamfara sun kashe 13

Ya ce:

“Da ta bincika sai ya bayyana mata cewa mutanen ne suka yaudare shi suka yi ta lalata da shi ta dubura a lokuta da dama, sakamakon haka ne ya kamu da ciwon cikin.”

Kiyawa ya kara da cewar an garzaya da matashin Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase, da ke Kano inda aka yi masa jinya aka kuma sallame shi.

A cewarsa bayan Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya da ba da umarni, an kamo wadanda ake zargin sun kuma amsa cewa sun aikata laifin.

Ya bayyana cewa daya daga cikin mutanane mai shekara 33 ya bayyana wa ’yan sanda cewa shi ne ya fara yaudarar yaron ya yi lalata da shi.

Jami’in dan dan sandan ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kafin a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

A wani labari na daban, jami'an hukumar hana fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Benuwai sun kama wata mata 'yar shekara 36, Chioma Afam, tare da abokiyar aikinta, Peace Caleb, mai shekara 22.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Afam, wacce take amfani da sunaye da dama kuma take sanye da hijabi domin guje wa binciken tsaro, an ce an kama ta tare da abokiyar cin mushen nata ne yayin da suke kokarin safarar kwayoyin Diazepam da Exol-5 guda 296,000 daga Onitsha a jihar Anambra, zuwa jihar Gombe.

Daraktan yada labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ya tabbatar da kamun a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel