Wata Sabuwa: Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Sake Tsunduma Yajin Aiki, Ta Fadi Dalili

Wata Sabuwa: Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Sake Tsunduma Yajin Aiki, Ta Fadi Dalili

  • Ƙungiyar malaman jami'o'i ASUU ta yi barazanar sake tsunduma yajin aiki bisa gazawar gwamnatin tarayya
  • Ƙungiyar tace har zuwa yanzun gwamnati biyu kacal cikin takwas na yarjejeniyar (MoU) ta iya aiwatar wa
  • ASUU ta zargi gwamnatin da cire wasu malamai daga tsarin biyan albashi, yayin da wasu kuma suke samun wani yanki na haƙƙinsu

Malaman jami'o'i ka iya komawa yajin aiki bayan gwamnatin tarayya da gaza cika yarjejeniyar da ta cimmawa da ƙungiyar ASUU, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Shugaban ƙungiyar reshen jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa, Bauchi (ATBU), Ibrahim Inuwa, yace:

"Cikin yarjejeniya takwas da aka amince da su a baya, biyu kacal gwamnatin tarayya da cika musu."

ASUU zata sake tsunduma yajin aiki
Wata Sabuwa: Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Sake Tsunduma Yajin Aiki, Ta Fadi Dalili Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Inuwa ya bayyana cewa sauran shida da gwamnati ta gaza aiwatarwa sun haɗa da biyan alawus ɗin malaman jami'a, samar da kuɗaɗe domin farfaɗo da jami'o'i, ƙara yawan jami'o'in jiha, sake zama teburin shawarwari da kuma maye tsarin biyan albashi IPPIS da wanda ASUU ta gabatar UTAS.

Kara karanta wannan

Karo na Shida a Jere, FG Ta Sake Kara Wa'adin Hada Layin Waya da NIN, Ta Fadi Dalili

Ya ƙara da cewa lokacin biyan alawus ɗin malaman jami'a (EAA) na watan Mayu ya shuɗe kuma gwamnati ta yi gum a kan lamarin, kamar yadda punch ta ruwaito.

Babu kwanciyar hankali a makarantu

Shugaban ASUU-ATBU yace a halin yanzun babu kwanciyar hankali a jami'o'in ƙasar nan, kuma akwai barazanar sake kulle jami'o'in. Yace:

"Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta gaza aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da aka cimma wanda ya kawo ƙarshen yajin aikin ASUU a watan Disamba 2020."

Ana Zabtarewa malamai albashi

Mr. Inuwa ya cigaba da cewa ofishin Akanta Janar na ƙasa, ta hanyar ofishin tsarin biyan albashi IPPIS sun cigaba da zare mambobin ASUU daga biyan albashi yayin da wasu suke samun wani yanki na albashinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel