Lauya ya bayyana laifuka 3 da gwamnatin Buhari ke tuhumar Sunday Igboho akai

Lauya ya bayyana laifuka 3 da gwamnatin Buhari ke tuhumar Sunday Igboho akai

  • Babban lauyan dake kare Sunday Igboho ya bayyana laifukan da gwamnati ke tuhumarsa da shi
  • A baya an kame Sunday Igboho a jamhuriyar Benin, yayin da ake kokarin mika shi ga gwamnatin Najeriya
  • Lauyan ya bayyana tuhuma uku yayin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta BBC Yoruba

Babban mai ba da shawara ga Sunday Igboho, mai tayar da zaune tsaye kuma dan awaren Yarbawa, Ibrahim Salami, ya bayyana abin da gwamnatin Najeriya ta fada wa takwararta ta Jamhuriyar Benin don ba da sammacin kame da kuma yiwuwar mika Igboho.

Salami ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta zargi Igboho da safarar makamai zuwa Najeriya, SaharaReporters ta ruwaito.

Da yake magana da BBC Yoruba, lauyan ya ce gwamnatin Najeriya ta kuma zargi Igboho da kiran aware da kuma tayar da hankalin kasar.

Lauya ya bayyana laifuka 3 da gwamnatin Buhari ke tuhumar Sunday Igboho akai
Sunday Igboho, dan awaren Yarbawa | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Salami ya ce:

“Gwamnatin Najeriya ta ce Igboho yana da hannu a safarar makamai zuwa Najeriya.

Kara karanta wannan

‘Muna rokon Ubangijinmu ya yi mana maganin Buhari’ - Ayo Adebanjo kan kamun Igboho

Na biyu shi ne yana haifar da hargitsi a Najeriya na uku kuma shi ne yana kokarin raba Najeriya gida biyu ko uku.”

Kotu ta yi hukunci kan Sunday Igboho, ta kuma saki matarsa

Wata kotu mai suna Cour De’appal De Cotonou, Jamhuriyar Benin, inda aka gurfanar da dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo (Igboho) da matarsa a ranar Alhamis, ya ba da umarnin a saki matar da yammacin yau.

SaharaReporters ta samu labarin daga jami’an kotun cewa kotun ta yanke hukuncin cewa a mayar da Igboho zuwa gidan yari.

Wani jami'i ya ce:

“Sun gama zaman kotu. Matar za a sake ta a daren yau kuma Sunday zai ci gaba da kasancewa a tsare. An dage batun har zuwa ranar Juma’a.”

Kotu a Benin ta sa ranar yanke shawarin mika Sunday Igboho Najeriya

Wata kotu a Jamhuriyar Benin ta tsayar da ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli, don fara sauraron shari’ar da ake yi wa Sunday Igboho, dan awaren Yarbawa.

Kara karanta wannan

FG bata mika bukatar dawo da Igboho Najeriya ba yayin da kotu a Kwatano ta tsare shi

Mai magana da yawun Igboho, Olayomi Koiki ne ya bayyana shirin sauraren karar a ranar Laraba, 21 ga watan Yuli, in ji PM News.

Dan awaren Yarbawan, wanda har yanzu ke hannun Brigade criminelle a Cotonou zai san makomarsa yayin sauraron karar, jaridar The Nation ta kara da cewa.

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa za a kara himma don zakulo wadanda ke dagula zaman lafiyar kasar da barazana ga 'yan kasar.

Ya bayar da wannan tabbacin ne 'yan sa'o'i bayan da aka kama wani dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda ake kira Sunday Igboho.

Hukumar 'Yan Sanda ta Kasa da Kasa (Interpol) ta kame Igboho a Cotonou, Jamhuriyar Benin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Buhari, duk da bai yi magana kai tsaye ba game da kamun Igboho, ya ba da tabbacin zakulwar ne a garinsa na Daura ta Jihar Katsina, bayan Sallar Idin Layya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu ta yi hukunci kan Sunday Igboho, ta kuma saki matarsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel