Da Dumi-Dumi: Kotu ta yi hukunci kan Sunday Igboho, ta kuma saki matarsa
- Bayan zaman kotu, an sake tura Sunday Igboho magarkama don sake saurarar kara a karo na biyu
- Kotu ta amince da sakin matar Sunday Igboho yayin da ta bukaci ci gaba da ajiye Igboho a kasar
- An kame Sunday Igboho a jamhuriyar Benin, inda ake kokarin mika shi ga gwamnatin Najeriya bisa wasu laifuka
Wata kotu mai suna Cour De’appal De Cotonou, Jamhuriyar Benin, inda aka gurfanar da dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo (Igboho) da matarsa a ranar Alhamis, ya ba da umarnin a saki matar da yammacin yau.
SaharaReporters ta samu labarin daga jami’an kotun cewa kotun ta yanke hukuncin cewa a mayar da Igboho zuwa gidan yari.
Wani jami'i ya ce:
“Sun gama zaman kotu. Matar za a sake ta a daren yau kuma Sunday zai ci gaba da kasancewa a tsare. An dage batun har zuwa ranar Juma’a.”
Kotu a Benin ta sa ranar yanke shawarin mika Sunday Igboho Najeriya
Wata kotu a Jamhuriyar Benin ta tsayar da ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli, don fara sauraron shari’ar da ake yi wa Sunday Igboho, dan awaren Yarbawa.
Mai magana da yawun Igboho, Olayomi Koiki ne ya bayyana shirin sauraren karar a ranar Laraba, 21 ga watan Yuli, in ji PM News.
Dan awaren Yarbawan, wanda har yanzu ke hannun Brigade criminelle a Cotonou zai san makomarsa yayin sauraron karar, jaridar The Nation ta kara da cewa.
Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa za a kara himma don zakulo wadanda ke dagula zaman lafiyar kasar da barazana ga 'yan kasar.
Ya bayar da wannan tabbacin ne 'yan sa'o'i bayan da aka kama wani dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda ake kira Sunday Igboho.
Hukumar 'Yan Sanda ta Kasa da Kasa (Interpol) ta kame Igboho a Cotonou, Jamhuriyar Benin, jaridar Daily Trust ta ruwaito. Buhari, duk da bai yi magana kai tsaye ba game da kamun Igboho, ya ba da tabbacin zakulwar ne a garinsa na Daura ta Jihar Katsina, bayan Sallar Idin Layya.
Asali: Legit.ng