‘Muna rokon Ubangijinmu ya yi mana maganin Buhari’ - Ayo Adebanjo kan kamun Igboho

‘Muna rokon Ubangijinmu ya yi mana maganin Buhari’ - Ayo Adebanjo kan kamun Igboho

  • Shugaban Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ya caccaki gwamnatin Buhari sakamakon kamen Igboho
  • Ya ce Buhari na dogaro da ‘yan barandan jami’an tsaron kasa; yayin da suke dogaro da Allah
  • Sannan ya ce gwamnatin tarayya ba ta da hurumin neman a taso kyayar Igboho daga Jamhuriyar Benin

Ayo Adebanjo, shugaban kungiyar Afenifere, kungiyar Yarbawa zalla kan zamantakewa da siyasa, ya ce gwamnatin tarayya ba ta da hurumin neman a dawo da Sunday Igboho daga Jamhuriyar Benin.

Ya roki "Allah da Yayi musu maganin Buhari".

Bayan 'yan makonni bayan da jami'an tsaro na farin kaya (DSS) suka bayyana neman Ighoho "ruwa a Jalo", jami'an tsaron Jamhuriyar Benin sun kame shi a birnin Cotonou yayin da yake kokarin tsere wa zuwa Jamus.

Mahukuntan Najeriya na ci gaba da matsa kaimi wajen ganin an dawo da dan rajin neman kafa kasar Yarbawa daga kasar ta Benin mai makwabtaka.

Kara karanta wannan

Kanu da Igboho: Kungiyar arewa ta dau zafi, ta bayyana abun da ya kamata FG ta yi wa ‘yan bindiga da makiyaya

Kamun na Igboho ya haifar da martani daga fitattun mutane a Najeriya, musamman daga yankin Kudu maso Yammacin kasar.

Kungiyar Manoma ta Agbekoya ta ce a shirye take da ta yi yaki kwato 'yancin Igboho" yayin da suke cewa "babu abin da zai same shi".

‘Muna rokon Ubangijinmu ya yi mana maganin Buhari’ - Ayo Adebanjo
‘Muna rokon Ubangijinmu ya yi mana maganin Buhari’ - Ayo Adebanjo kan kamun Igboho Hoto: Pa Adebanjo
Asali: Twitter

A ranar Alhamis, a cikin hira da tashar Arise TV, Adebanjo ya daga muryarsa ga masu yin martani kan kamen Igbohon.

Ya bayyana Igboho a matsayin "fursunan siyasa", kuma ya ce gwamnatin tarayya ba ta da ''izinin neman tasa keyarsa zuwa Najeriya.’

Gwamnatin Najeriya tsoron Sunday Igboho suke

Shugaban na Afenifere mai shekara 93 ya ce hukumomin Najeriya kawai suna tsoro da fargabar shaharar Igboho ne kawai, yana mai cewa "mahukunta na son kashe shi saboda yana jagorantar tawayen jama'a".

Ya ce,

“Buhari na iya dogaro da ‘yan kanzaginsa, amma mu muna da Allah. Kuma muna kira ga Allahnmu da Ya yi mana maganin Buhari ”.
“Shi [Igboho] dan gudun hijirar siyasa ne. Bai aikata wani laifi a nan. Bai jagoranci kashe kowa ba. Bai tserewa kowa ba bayan aikata laifi. Ya gudu domin ransa saboda masu iko na son kashe shi saboda fafutikar da yake yi. Yana kuma jagorantar wani tawayen da al’umma ke yi, ”in ji Adebanjo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel