Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan hukuncin harbe 'yan bindiga a Najeriya

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan hukuncin harbe 'yan bindiga a Najeriya

  • Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana matsalar da Najeriya ke fuskanta a yanzu
  • Ya ce bindiga ko harsasai ba za su iya magance matsalar 'yan bindiga da 'yan fashi da makami ba
  • Ya ce gwamnati na bukatar sake sabon shiri da kirkiro dabaru domin yakar wadannan munanan ayyuka

Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya ce harsasai da sauran karfin makamai su kadai ba za su iya dakatar da fashi da makami, bindiganci da sauran nau'ikan aikata laifuka a kasar ba.

Ya fadi haka ne a ranar Lahadi a Abuja yayin bikin cikar shekaru 50 na tsohon Corps Marshal na Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayya (FRSC) kuma Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Osita Chidoka.

A cewarsa, magance ta'addanci da aikata laifuka yana bukatar manyan shirye-shirye masu inganci na gwamnati, fasaha da sauran dabaru, Reuben Abati ya tattaro.

KARANTA WANNAN: Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan sanda a Zamfara sun kashe 13

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan batun harbe 'yan bindiga da ake yi
Tsohon shugaban kasan Najeriya Goodluck Jonathan | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Ya ce:

“Tare da yawaitar fashi da makami da sauran laifukan dake faruwa a yanzu ya nuna karara cewa harsasai kadai ba za su iya dakatar da shi ba ko wasu ayyukan laifi a cikin 'yan Adam.
"Yana bukatar manyan shirye-shirye masu inganci na gwamnati, yana bukatar fasaha, yana bukatar abubuwa da yawa don dakatar da fashi da makami da duk nau'ikan laifuka, hade da cin hanci da rashawa da muke magana akai a kowace rana."

Ya ce yayin da gwamnatoci ke kashe ‘yan fashi da makami, wasu kuma suna fashin aljihu a cikin fage daya kuma irin al’ummar da 'yan kasa ke ciki kenan a yau.

Ya ce abubuwa suna kara rikicewa tare da gabatar da fasahar sadarwa wanda ke mulkin duniya a yanzu, don haka akwai bukatar a yi aiki tare don dakile yawaitar aikata laifuka.

Ranar da aka fara harbe 'yan fashi da kamai a Najeriya

Jonathan, ya lura cewa ranar da aka haifi Osita ita ce ranar da aka fara harbe ‘yan fashi da makami a Najeriya.

Daily Trust ta rawaito cewa kisan farko a bainar jama'a a Najeriya ya faru ne a Bar Beach a watan Yulin 1971, lokacin da aka harbe wani Babatunde Folorunsho, saboda fashi da makami.

Hakazalika a ranar aka harbe Joseph Ilobo da Williams Alders Oyazimo, wani karamin Laftanal a rundunar Sojan Ruwan Najeriya.

Jonathan ya ce:

“(Wannan shine) Kwanan wata mai ban mamaki. Ranar da aka haife ka (Osita) ita ce ranar da aka fara harbe ‘yan fashi da makami a Najeriya, hakan babban abu ne sosai.
"Abu na musamman. Sa'ar al'amarin shine kai ba dan fashi da makami bane. Amma lokaci ya wuce lokacin da ake harbe 'yan fashi da makami.

KARANTA WANNAN: Babbar Sallah: Gwamnatin Sokoto ta gwangwaje marayu da makudan miliyoyi

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

A wani labarin, Akalla jami'an Kwastam uku da wani soja sun ji rauni lokacin da wasu masu fasa kwauri suka far musu a yankin Igboora da ke karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo a ranar Juma'a.

Theophilus Duniya, Jami’in Hulda da Jama’a na Kwastam, sashin Ayyuka na Tarayya, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar kuma ya ba manema labarai a Ibadan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Duniya ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na daren Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel