Babbar Sallah: Gwamnatin Sokoto ta gwangwaje marayu da makudan miliyoyi

Babbar Sallah: Gwamnatin Sokoto ta gwangwaje marayu da makudan miliyoyi

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta gwangwaje marayu a jihar ta Sokoto gabanin babbar sallah mai zuwa
  • Gwamnatin jihar ta ware wasu kudade domin sayen shanu ga gundumomi 87 dake fadin jihar ta Sokoto
  • Rahoto ya bayyana gwamnati ta kasafta yadda za a saya wa marayu a dukkanin gundumomin shanu

Gwamnatin Jihar Sokoto ta raba Naira miliyan 21.7 ga gundumomi 87 don sayan shanun sallah ga marayu, Daily Trust ta ruwaito.

An ba kowace daga cikin gundumomin N200,000 na sayen saniya da kuma N20,000 don jigilar ta.

A yayin kaddamar da bayarwar, Sultan na Sokoto, Muhammad Sa’ad Abubakar Said, ya gode wa gwamnatin jihar bisa ci gaba da wannan aikin duk da raguwar albarkatun ta.

A cewarsa, wannan zai ba marayun damar jin su ma ana damawa dasu.

KARANTA WANNAN: Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17000 a sansani a jihar Borno

Babbar Sallah: Gwamnatin Sokoto ta gwangwaje marayu da makudan miliyoyi
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya bukaci hakiman yankunan da su tabbatar da gaskiya da adalci wajen sauke wannan nauyi da aka daura musu.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Ya yi kashedin cewa:

“Don haka, ina bukatar dukkanku da ku guji ko ma kokarin yin amfani da kudin don ayyukan karan kanku. Idan baku kara ba to kar ku rage."

Tun da farko, Malam Muhammad Maidoki, Shugaban Hukumar Zakka da Ba da Tallafi ta Jihar Sokoto, ya yaba wa hakiman yankunan bisa jajircewar da suka nuna wajen gudanar da aikin.

Gwamna Zulum ya biya ma'aikata albashi, ya rabawa gajiyayyu kudade

A ci gaba da shirye-shiryen babbar sallah mai zuwa, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya amince da biyan dukkan albashin watan Yuli nan take ga dukkan ma'aikatan gwamnati a fadin jihar., Vanguard ta ruwaito.

Hakazalika gwamna Zulum ya fitar da sama da N100m don rabawa bangarori daban-daban na Mutanen da ke fama da nakasa (PLWDs).

Sama da Naira N100m ga masu karamin karfi a matsayin wani bangare na abinda Gwamnati mai ci yanzu ta kirkiro, wanda galibi Kwamishinan Wasanni da Ci gaban Matasa, Hon Saina Buba ke rabawa.

Kara karanta wannan

Kotun Najeriya ta yankewa wasu tsoffin ‘yan sanda biyu hukuncin kisa saboda garkuwa da wani mutum

KARANTA WANNAN: An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Babbar Sallah: An shawarci masarautar Kano da wasu masarautu su soke hawan sallah

A wani labarin, Kwamatin yaki da cutar korona na Gwamnatin Tarayyar Najeriya ya saka jihohi shida da kuma Abuja cikin mafiya hadarin yaduwar cutar sannan ya shawarce su da su soke bukukuwan Babbar Sallah, BBC Hausa ta ruwaito.

Shugaban kwamatin Presidential Steering Committee (PSC) kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a daren Asabar.

Ya zayyana jihohin kamar haka: Legas, Kano, Kaduna, Oyo, Rivers, Filato da Abuja. Mista Mustapha ya ce shi kansa fitar da jerin sunayen mataki ne na yaki da yaduwar cutar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.