Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan sanda a Zamfara sun kashe 13

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan sanda a Zamfara sun kashe 13

  • Wani rahoto da Legit.ng Hausa ta samo ya nuna cewa, 'yan bindiga sun hallaka wasu jami'an 'yan sanda a Zamfara
  • Rahoton ya ce lamarin ya faru ne bayan da sojoji suka fatattaki 'yan bindigan a wani yankin jihar
  • An ce mutane 13 sun hallaka yayin harin na 'yan bindiga, kuma tuni suka gudu bayan gama barnar

A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kashe 'yan sanda 13 da wasu mutum uku a wani hari da suka kai garin Kurar Mota da ke karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

Mazauna garin sun shaida cewa tun da farko mutanen sun yi yunkurin mamaye garin Magami, wani yanki dake da tazarar kilomita 50 kudu da Gusau, babban birnin jihar, amma sojoji suka fatattake su.

KARANTA WANNAN: Babbar Sallah: Gwamnatin Sokoto ta gwangwaje marayu da makudan miliyoyi

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun hallaka jami'an 'yan sanda 13 a jihar Zamfara
'Yan bindiga dauke da makamai | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Twitter

Wani mazaunin garin mai suna Kabir Dansada ya fada wa Daily Trust cewa:

Kara karanta wannan

Fusatattun matasa sun kurmushe mutum 5 da ake zargin 'yan bindiga ne a Edo

“Sun janye bayan da sojojin dake wurin suka ci karfinsu. Daga nan suka yi tattaki zuwa wata al'umma dake kan hanyar Magami - Dankurmi - Dangulbi suka kashe mutum daya kuma suka kone shaguna hudu.”
“Daga baya, sai suka koma garin Kurar Mota kuma suka kai hari kan sansanin 'yan sanda kusa da asibitin garin. Daga nan sai 'yan ta'addan suka fantsama cikin daji ”
“An kai jami’an da aka kashe da wadanda suka jikkata zuwa Gusau a cikin ayarin motocin 'yan sanda da yammacin yau. Na ga motocin ‘yan sanda da dama suna zirga-zirga zuwa yankin."

Har yanzu ba ji ta bakin 'yan sanda ba, duk da cewa an tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar SP Muhammad Shehu.

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Akalla jami'an Kwastam uku da wani soja sun ji rauni lokacin da wasu masu fasa kwauri suka far musu a yankin Igboora da ke karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Theophilus Duniya, Jami’in Hulda da Jama’a na Kwastam, sashin Ayyuka na Tarayya, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar kuma ya ba manema labarai a Ibadan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Duniya ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na daren Juma'a.

KARANTA WANNAN: Yadda Gwamnati Ta Kame Sheikh Abduljabbar, Ta Turashi Magarkama Ya Yi Sallah

Kotun Najeriya ta yankewa wasu tsoffin ‘yan sanda biyu hukuncin kisa saboda garkuwa da wani mutum

A wani labarin, Babbar kotun jihar Akwa Ibom ta yanke wa wasu ‘yan sanda biyu hukuncin kisa saboda yin garkuwa da wani dillalin shanu mazaunin Uyo, mai suna Alhaji Muhammed Umar Barkindo.

‘Yan sandan da aka yanke wa hukuncin sun hada da Kofur Friday Udo, da kuma Saturday Okorie wadanda tuni aka sallame su daga rundunar ‘yan sanda ta Najeriya, jaridar The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya kai hari kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa

Kotun da ke zaune a karamar hukumar Ikot Ekpene ta jihar ta kuma yanke hukuncin kisa ga wasu mutum uku, Walter Udo, Ibiono Ibom, da Udo Etim wadanda aka yi amfani da gidansu don ajiye wanda aka yi garkuwa da shi, yayin da suke neman fansar naira miliyan 100.

Asali: Legit.ng

Online view pixel