2023: Fitaccen jagoran Ibo ya yi hasashen abun da zai faru idan Tinubu ya zama shugaban Najeriya

2023: Fitaccen jagoran Ibo ya yi hasashen abun da zai faru idan Tinubu ya zama shugaban Najeriya

  • Gabanin zaben 2023, wani dan siyasar Ibo mazaunin Legas, Joe Igbokwe ya ce abubuwa za su yi kyau idan Tinubu ya zama shugaban kasa
  • Igbokwe wanda shine hadimin gwamna Sanwo-Olu na musamman kan magudanan ruwa da albarkatun ruwa ya kuma ce yankin kudu ne ya kamata ya samar da shugaban kasa amma bai san takamaiman shiyyar ba
  • Fitaccen dan siyasar ya ce kamata ya yi ace zagayen yankin kudu maso gabas ne idan da yankin ya buga siyasar yadda ta dace

Joe Igbokwe, mai ba gwamnan jihar Legas shawara na musamman kan magudanan ruwa da albarkatun ruwa, ya ce "abubuwa zasu inganta" idan Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban Najeriya.

Igbokwe, jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, ya fadi hakan ne yayin amsa tambayoyi a wata hira da ya yi da BBC Pidgin.

KU KARANTA KUMA: Ta’addanci: Mataimakin gwamnan Zamfara ya shiga gagarumin matsala bayan gangamin PDP

Kara karanta wannan

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Shugaban PDP na kasa da Gwamna Wike

2023: Fitaccen jagoran Ibo ya yi hasashen abun da zai faru idan Tinubu ya zama shugaban Najeriya
Joe Igbokwe ya ce abubuwa za su fi kyau a Najeriya idan jagoran APC, Bola Tinubu, ya zama shugaban Najeriya Hoto: BOLA Tinubu Ambassadors Southwest, Joe Igbokwe
Asali: Facebook

Da aka tambaye shi ko yana ganin Tinubu, babban jigon jam’iyyar APC na kasa, a matsayin wanda zai iya zama shugaban kasa, sai ya ce:

"Idan ya zama shugaban kasar nan, abubuwa za su yi kyau. Abubuwa za su daidaita. Shi magini ne. Shi ya gina tushen bunkasar Legas. Kuma yanzu Lagos ita ce ta biyar mafi karfin tattalin arziki a Afirka. Don haka zai iya agazawa.
"Ya kasance babban akawu. Ya yi aiki tare da Mobil. Ya mulki Legas. Ya kasance sanata. Yana da abubuwa da yawa da zai kawo ci gaba. Ka sani, ba a iya koyon kwarewa daga littattafai kadai. Don haka, yana da abubuwa da yawa da zai kawo ci gaba. Amma 'yan Najeriya ne za su yanke hukunci."

Duk da cewa bai fito fili ya bayyana kudirinsa ba, ana yada jita-jitar cewa Tinubu yana da sha'awar ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Ya kamata Kudancin Najeriya ya samar da shugaban kasa a 2023

A hirar wanda kuma aka wallafa a Facebook, Igbokwe ya ce ya yi imanin cewa zagayen yankin kudu ne ya samar da shugaban Najeriya bayan karewar wa'adin Shugaba Buhari a 2023.

KU KARANTA KUMA: Matawalle: PDP ta ce lallai sai an rantsar da mataimakin gwamnan Zamfara a matsayin gwamna

Muna da fahimta, yarjejeniyar dattako tsakanin arewa da kudu. Don haka, mulki na zuwa kudu amma ban san inda zai je ba.

Ya ce kamata ya yi mulkin ya je yankin kudu maso gabas idan da yankin ya buga siyasa yadda ya dace. Sai dai ya ce yankin da 'yan kabilar Ibo suka fi yawa sun hada kai da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da kin yin mu'amala da sauran mutane.

Da aka tambaye shi ko wani lokaci zai zo da Najeriya za ta samu shugaban kasar Ibo, Igbokwe ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

"Zai iya zama nine idan lokaci ya yi. Mai yiwuwa ne amma sai mutum ya buga siyasa. Dole mutum ya gina gadojin.”

Yankin mu ya kamata ya fitar da shugaban kasa na gaba, Gwamnonin Kudu

A baya mun ji cewa gwamnonin jihohin kudancin Nigeria 17 sun amince kan cewa shugaban kasar Nigeria na gaba a shekarar 2023 ya kamata ya fito daga yankinsu ne kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Hakan na dauke ne cikin sakon bayan taro da kungiyar gwamnonin kudun ta fitar bayan taron ta da aka yi a gidan gwamnatin Legas da ke Alausa, ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa sun kuma cimma matsayar cewa ya kamata a rika kama-kama ne tsakanin kudu da arewa wurin zaben shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel