Ta’addanci: Mataimakin gwamnan Zamfara ya shiga gagarumin matsala bayan gangamin PDP
- Yan kwanaki bayan sauya shekar gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, alamu sun nuna mataimakinsa, Mahdi Aliyu Muhammad Gusau, yana fuskantar wasu matsaloli
- A ranar Laraba, 14 ga watan Yuli ne aka aika sammaci ga Gusau kan ya bayyana a gaban majalisar dokokin jihar tare da kwamishinan ‘yan sanda, Hussaini Rabiu
- Wannan sammacin na zuwa ne a kan wani gangamin siyasa da mataimakin gwamnan ya shirya kwana daya bayan ‘yan bindiga sun kai wasu manyan hare-hare a wasu garuruwa
An aika sammaci ga mataimakin gwamnan Zamfara, Mahdi Aliyu Muhammad Gusau don ya bayyana a gaban majalisar dokokin jihar a ranar Talata, 27 ga watan Yuli.
'Yan majalisar jihar sun fusata a ranar Laraba, 14 ga watan Yuli, kan cewa Gusau ya ci gaba da gudanar da taron siyasa a daidai lokacin da ayyukan ‘yan fashi ke karuwa a jihar, Channels TV ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Matawalle: PDP ta ce lallai sai an rantsar da mataimakin gwamnan Zamfara a matsayin gwamna
Tushen sammacin
Da yake daukar nauyin kudirin, Hon Yusuf Alhassan Kanoma mai wakiltar Maru ta Arewa, ya bayyana cewa ya kamata mutumin da ake girmamawa sosai kamar mataimakin gwamna ya sani fiye da jefa rayuwar ‘yan kasa cikin hadari, Daily Trust ta kuma ruwaito.
Alhassan ya yi watsi da rashin bin tsarin mulkin dimokiradiyya na Gusau, inda ya bayyana cewa abin kunya ne bayan an fahimci cewa ya fi nuna damuwa da ra’ayin siyasarsa da kuma burinsa a lokaci mai hatsari inda duk jihar ke zaman makokin kisan da aka yi wa dimbin mazauna kauyuka a cikin garuruwa kusan biyar.
KU KARANTA KUMA: Abokan ango sun rikirkita aurensa, suna ta jifan mutane da bandir-bandir din kudi a cikin wani bidiyo
Kaakakin majalisar, Honorabul Nasiru Mu’azu Magarya ya amince da kudirin dan majalisar inda ya bayyana cewa dole ne a aika makamancin wannan sammacin ga kwamishinan ‘yan sanda, Hussaini Rabiu.
Ba zan yi butulci ba, ba zan koma APC ba: Mataimakin gwamnan Zamfara
A gefe guda, Legit.ng ta kawo a baya cewa mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Gusau, ya lashi takobin cewa zai cigaba da zama a jam'iyyar People’s Democratic Party PDP, duk da cewa gwamnan jihar, Bello Matwalle ya koma All Progressives Congress APC.
Dukkan Sanatocin Zamfara uku, yan majalisar wakilai shida da yan majalisa jiha 24 sun sauya sheka tare da gwamnan illa mataimakinsa.
Muhammad Gusau ya ce zai cigaba da kasancewa da PDP saboda jama'ar PDP suka tsaya da su lokacin da suke cikin bukata, rahoton Daily Trust.
Asali: Legit.ng