Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto
- Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya sha alwashin rushe kauyen Remon a jihar Sokoto
- An tattaro cewa kauyen Remon ya kasance maboyar bata-gari da miyagu
- Tambuwal ya ziyarci kauyen a yau Talata, 13 ga watan Yuli, inda ya ce mazauna yankin na zaune ba bisa ka’ida ba
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana shirin rusa kauyen Remon da ke karamar hukumar Dange Shuni na jihar Sokoto.
Wannan ya biyo bayan binciken jaridar Daily Trust da aka buga a ranar Lahadi wanda ya fallasa duk haramtattun ayyukan da ake gudanarwa a yankin.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Jerin sunayen kwamishinonin INEC 5 da majalisar dattijai ta tabbatar da su
Tambuwal, wanda ya ziyarci yankin da misalin karfe 11:30 na safiyar ranar Talata, 13 ga watan Yuli, ya ce akasarin mazaunan kauyen na zaune ne ba bisa ka’ida ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jami'an tsaro sun kai samame kauyen Remon a ranar Asabar, inda suka kame sama da mutum 100 da ake zargi.
Aikin ya hada da sojoji, Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), hukumar kwastam ta Najeriya, hukumar kiyaye haddura ta kasa, Ma’aikatar harkokin waje, jami’an tsaro na farin kaya da NSCDC karkashin jagorancin ‘yan sanda suka jagoranta.
Rahotanni sun ce samamen wanda aka fara shi da misalin karfe biyar na yamma ya shafe kusan sa’o’i biyu.
An tura wadanda ake zargin zuwa hedikwatar 'yan sanda sannan aka ajiye su a sashin binciken manyan laifuka na rundunar.
Jaridar Aminiya ta kuma ruwaito cewa daga cikin wadanda ake zargin har da mata.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya shirya liyafar cin abincin dare tare da sanatoci 109 a yau Talata
Da yake tabbatar da aikin, kakakin rundunar, ASP Sanusi Abubakar, ya ce an kama mutane 144 da ake zargi tare da kwato kwayoyi da yawa a yayin samamen.
Ya ce:
“Za mu binciki dukkansu, kuma duk wanda muka gano yana da laifi za mu gurfanar da shi a gaban kuliya.”
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci mambobin majalisar dattijai zuwa liyafar cin abincin dare a Fadar Shugaban Kasa a yau Talata, 13 ga watan Yuli da karfe 8 na dare.
Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar shugaban kasar a zauren majalisar yayin fara zama, jaridar Punch ta ruwaito.
Lawan ya bukaci takwarorinsa da su zo bangaren majalisar dattijai ta kasa don tashi zuwa fadar Villa da karfe 7 na yamma.
Asali: Legit.ng