Yankin mu ya kamata ya fitar da shugaban kasa na gaba, Gwamnonin Kudu
- Kungiyar gwamnonin jihohin Kudu 17 na Nigeria ta ce yankinta ne ya kamata ya fitar da shugaban kasa a 2023
- Gwamnonin sun bayyana hakan ne bayan taron da suka gudanar a ranar Litinin a gidan gwamnatin jihar Legas
- Gwamnonin sun cimma matsayar cewa karba-karba ya kamata a rika yi tsakanin kudu da arewa wurin fitar da shugaban kasa
Gwamnonin jihohin kudancin Nigeria 17 sun amince kan cewa shugaban kasar Nigeria na gaba a shekarar 2023 ya kamata ya fito daga yankinsu ne kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Hakan na dauke ne cikin sakon bayan taro da kungiyar gwamnonin kudun ta fitar bayan taron ta da aka yi a gidan gwamnatin Legas da ke Alausa, ranar Litinin.
DUBA WANNAN: Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo
Daily Trust ta ruwaito cewa sun kuma cimma matsayar cewa ya kamata a rika kama-kama ne tsakanin kudu da arewa wurin zaben shugaban kasar.
Gwamnan jihar Ondo kuma shugaban kungiyar gwamnonin na kudu, Arakunrun Oluwarotimi Akeredolu ya jadada matsayin kungiyar na yin siyasa na adalci da rashin nuna banbanci.
Kazalika, ya kuma ce kungiyar tana goyon bayan hadin kan Nigeria a matsayin kasa daya amma bisa adalci, cigaba da zaman lafiya tsakanin mazauna kasar.
KU KARANTA: Da Duminsa: Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga a Makarantar Fasto Oyedepo a Kaduna
Kungiyar ta yi nazari kan harkar tsaro a kasar nan inda ta jinjinawa hukumomin tsaro bisa jajircewarsu wurin ganin an samu tsaro da zaman lafiya yayin da suka jajantawa iyalan wadanda suka rasa ransu yayin aiki.
Ba da Jimawa Ba Wasu Gwamnonin PDP Zasu Biyo Mu Zuwa APC, Gwamnan Ebonyi
Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa akwai wasu takwararonsu gwamnonin PDP da zasu sauya sheƙa zuwa APC ba da jimawa ba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Gwamnan ya faɗi hakane a wurin taron jiga-jigan jam'iyyar APC na jihar, wanda aka shirya domin tattaunawa kan yadda za'a gudanar da tarukan APC dake tafe a jihar.
Umahi, wanda bai jima sosai da sauya sheƙa zuwa APC ba, ya tabbatar da cewa ba zai bari a ƙayar da jam'iyyar a jihar Ebonyi ba.
Asali: Legit.ng