Kyawawan hotunan ‘yar Najeriya da ta yi wuf da wani Bature, jama’a sun yi cece-kuce

Kyawawan hotunan ‘yar Najeriya da ta yi wuf da wani Bature, jama’a sun yi cece-kuce

  • Wata ‘yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya yayin da hotunan aurenta suka bayyana
  • Matar wacce aka bayyana da suna Remy sun yi mubaya’ar aure da Baturen mijinta yayin da ma’auratan suka yi ado da kayansu na gargajiya
  • Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun taya sabbin ma'aurata murna yayin da wasu da dama suka yi sharhi mai ban dariya

Wata baiwar Allah ta hadu da cikar burinta a wurin wani dan kasar waje kuma sun yi aure a kwanan nan.

Matar mai suna Remy ta shiga daga ciki da burin zuciyarta wanda ya kasance Bature.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta amince da daurin shekaru 20 ga barayin akwatin zabe

Kyawawan hotunan ‘yar Najeriya da ta yi wuf da wani Bature, jama’a sun yi cece-kuce
Amarya da ango Hoto: @gossipmillnigeria
Asali: Instagram

A cikin hotunan da shafin @gossipmillnigeria ya wallafa a Instagram, an gano ma’auratan sanye da kaya iri daya.

Baturen da matar sun yi kyawawan hotuna cikin annashuwa da walwala a harabar wajen taron bikin.

Kara karanta wannan

Bidiyo ya nuna lokacin da mai martaba sarkin Kajuru ya fashe da kuka bayan masu satar mutane sun sako shi

'Yan Najeriya sun yi martani

Mutane da dama sun yaba da kyan da suka yi yayin da wasu ke ganin Baturen ya fi wasu ‘yan Najeriya kyau a cikin shigar gargajiyan.

@perry_linaa ta ce:

"Uwargida sarautar mata nagode da kika nuna mana hanya, don haka yanzu za mu iya auren su don samun shi."

KU KARANTA KUMA: Bidiyo ya nuna lokacin da mai martaba sarkin Kajuru ya fashe da kuka bayan masu satar mutane sun sako shi

@jazzilyn_gramm ya yi martani:

"Bari mu yi shiru dai, Baturen (ya hadu) shigar ta amshe shi fiye da wasu ‘Yan Najeriyan."

@shege_lee_wr ya ce:

"Abokan cinikin da kowa ke tattali .. ya kai kanki sai kika aure shi Remy ba haka ake yin abubuwa ba."

@cleopatra_dean_ ta yi martani:

"Ina taya ku murna, kun yi kokari, yaranku za su gode maku har abada saboda wannan babban sadaukarwa da kuka yi musu. Allah ya baku zaman lafiya a gidan aurenku."

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

Hotunan Wata Kyakkyawar Budurwa Yar Amurka da Ta Yi Wuf da Dan Najeriya

A gefe guda, a cewar masu iya magana "So ba ruwansa da yare ko ƙabila," wannan shaida ne yayin da wata kyakkyawar budurwa yar ƙasar Amurka, Janna Parker, ta canza sunanta zuwa, Janna Mofeyisola, bayan ta auri bayerabe, Owolabi Ikuejamoye.

Mrs Mofeyisola, ta garzaya shafinta na kafar sada zumunta domin shaida wa masu bibiyarta sabon cigaban da ta samu.

Ta rubuta a shafinta na LinkedIn cewa:

"Ina matuƙar farin cikin sanarwa ga babban shafin mu cewa zan canza sunana zuwa Janna Mofeyisola."

Asali: Legit.ng

Online view pixel