Hotunan Wata Kyakkyawar Budurwa Yar Amurka da Ta Yi Wuf da Dan Najeriya

Hotunan Wata Kyakkyawar Budurwa Yar Amurka da Ta Yi Wuf da Dan Najeriya

  • Wata santaleliyar yar ƙasar Amurka ta bayyana sabon sunan da ta canza bayan ta yi wuf da ɗan Najeriya
  • Matar mai suna, Janna Mofeyisola, ta canza sunan zuwa irin na yaren mijinta, Janna Ikuejamoye
  • Yan Najeriya sun taya ta murna yayin da wasu ma suka fara kiranta da ta zama tamkar yar cikinsu

A cewar masu iya magana "So ba ruwansa da yare ko ƙabila," wannan shaida ne yayin da wata kyakkyawar budurwa yar ƙasar Amurka, Janna Parker, ta canza sunanta zuwa, Janna Mofeyisola, bayan ta auri bayerabe, Owolabi Ikuejamoye.

KARANTA ANAN: Ina Jin Irin Raɗaɗin da Kuke Ji, Gwamna Ya Lallashi Mutanen Jiharsa

Mrs Mofeyisola, ta garzaya shafinta na kafar sada zumunta domin shaida wa masu bibiyarta sabon cigaban da ta samu.

Yat Amurka da ɗan Najeriya
Hotunan Wata Kyakkyawar Budurwa Yar Amurka da Ta Yi Wuf da Dan Najeriya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ta rubuta a shafinta na LinkedIn cewa: "Ina matuƙar farin cikin sanarwa ga babban shafin mu cewa zan canza sunana zuwa Janna Mofeyisola."

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

"Owolabi Ikuejamoye da kuma ni mun yi aure ranar 24 ga watan Afrilun wannan shekarar 2021 #rayuwaraure #Najeriya #yoruba."

Yan Najeriya sun taya ta murna

Wannan rubutun ya jawo mutane da dama suka fara tura mata saƙon taya murna a wurin da aka keɓe don yin magana.

Wasu yan Najeriya sun fara mata lale marhabun zuwa "al'adun yarbawa da suke na musamman."

Wasu daga cikin masu tofa albarkacin bakin su daga cikin yan Najeriya har sun fara kiranta da yarbanci 'Iyawo wa' wato matar mu.

KARANTA ANAN: Bikin Babbar Sallah: Mutane sun Koka Kan Yadda Farashin Dabbobin Layya Ya Yi Tashin Gwauron Zabi

Hotunan ma'auratan

Yar Amurka da ɗan Najeriya
Hotunan Wata Kyakkyawar Budurwa Yar Amurka da Ta Yi Wuf da Dan Najeriya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yar amurka ta yi wuf da ɗan Najeriya
Hotunan Wata Kyakkyawar Budurwa Yar Amurka da Ta Yi Wuf da Dan Najeriya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wani.labarin kuma Matsalar Tsaro: Na Damu Sosai da Yanayin Ƙuncin da aka Jefa Yan Kaduna a Ciki, El-Rufa'i

Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya bayyana cewa yana cikin matuƙar damuwa saboda halin ƙunci da al'umar Kaduna suke ciki wanda matsalar tsaro ta haifar a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

Gwamnan yace rahoton tsaro da aka gabatar ya nuna ainihin baƙin ciki da takaicin da rashin tsaro ya jawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel