Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

  • Mai girma Muhammadu Buhari ya zauna da ‘Yan Majalisar Tarayya a Aso Villa
  • Shugaban Najeriyar ya yi alkawarin kawo karshen masu tada zaune tsaye a kasar
  • Buhari ya yabi Majalisar da Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamilla suke jagoranta

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yi bakin kokarinta wajen ganin an kawo karshen matsalar rashin tsaro a duk fadin kasar nan.

Jaridar The Cable ta ce shugaban kasar ya bayyana wannan ne a lokacin da ya zauna da Sanatoci 109 da ‘yan majalisar wakilan tarayya 360 na kasar.

Da yake bayani a ranar Talata, 13 ga watan Yuli, 2021, shugaban Najeriyar ya yabi 'yan majalisar.

KU KARANTA: Tun 1914, ba a taba dacen da ya fi Buhari ba - Masari

Mu na fama da matsalar tsaro - Buhari

Femi Adesina ya rahoto shugaban kasar ya na cewa babban kalubalen da kasar nan ta ke fuskanta shi ne ta’adin ‘yan bindiga da masu tada kafar baya.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

“Rashin tsaro ya na zuwa mana da rigar ta’addanci, tada zaune-tsaye, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka a birane, wanda shi ne kalubalen da mu ka fi fama da shi.”
“Wasu daga cikin masu yin wannan danyen aiki, suna yi ne domin su samu wata riba, wasu kuma suna da wata rubabbiyar akida ne da su ke kai.”
“Duk abin da yake tunzura su, hakan barazana ne a matsayinmu na kasa.”

KU KARANTA: 'Yan Majalisa 469 za su ci abinci da Shugaban kasa

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa a Aso Villa
Buhari da 'Yan Majalisa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC
“A irin wannan yanayi, dole muyi duk abin da mu ke da iko, ba tare da damu wa da masu kauda mana hankali ba, mu kawo karshen barnar su, mu hukunta su.”

Aiki 'Yan Majalisar Tarayya ya na kyau

Daily Trust ta rahoto shugaban Najeriyar ya na cewa gwamnatinsa za ta yi nasarar kawo tsaro, sannan ya gode da irin gudumuwar da majalisa ta ke ba shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun gano rashin tasirin hada lamabobin SIM da NIN, ‘yan sanda ba sa iya bin sawun 'yan bindiga

Buhari ya yabi majalisar tarayya, ya ce ‘ya ‘yanta sun hadu wajen kawo cigaban kasa, ya gode da goyon-bayan da yake samu har daga ‘yan jam’iyyar hamayya.

Ba da dade wa ba ku ka ji cewa gwamnonin jihohin kudu maso yamma sun yi taro, kuma sun hadu da 'Yan majalisarsu a kan yadda za a canza tsarin mulki.

Gwamnonin shida sun yi tarayya a kan a rage karfin da gwamnatin tarayya ta ke da shi, sannan canza salo da tsarin kananan hukumomi da kason arzikin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel