Majalisar dattawa ta amince da daurin shekaru 20 ga barayin akwatin zabe

Majalisar dattawa ta amince da daurin shekaru 20 ga barayin akwatin zabe

  • Majalisar Dattijai ta amince da kudurin da ke neman a kafa Hukumar Hukunta Laifukan Zabe
  • Har ila yau, majalisar ta kuma amince da daure masu satar akwatin zabe shekara 20 a gidan yari
  • Hakan dai ya biyo bayan amincewa da rahoton da kwamitin Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya yake jagoranta

A jiya Laraba, 13 ga watan Yuli ne majalisar dattijai ta amince da kudurin da ke neman a kafa Hukumar Hukunta Laifukan Zabe.

Wannan ya biyo bayan la'akari da rahoton da Kwamitin majalisar kan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), wanda Sanata Kabiru Gaya (APC, Kano) ke jagoranta, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Majalisar dattawa ta amince da daurin shekaru 20 ga barayin akwatin zabe
Majalisar dattawa ta yi na'am da daurin shekaru 20 ga masu satar akwatin zabe Hoto: @DrAhamdLawan1
Asali: Facebook

Gaya, a cikin jawabinsa, ya ce kafa Hukumar Laifukan Zabe ya zama tilas duba da karancin hurumin da INEC ke da shi wajen gurfanar da masu aikata laifukan zabe kamar yadda sassa na 149 da 150(2) na Dokar Zabe ta kasa wacce aka yi wa kwaskwarima suka tanada.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Majalisar Dattawa a cikin doka ta 12 ta kudurin ta amince da daurin akalla shekaru biyar a gidan yari ko kuma tarar akalla Naira miliyan 10 ko kuma duka biyun, ga duk wani jami’i ko shugaban wata kungiya ko wata jam’iyya da ta tafka magudin zabe wanda ya saba wa tanade-tanade na 221, 225 (1) (2) (3) da (4) da 227 na Tsarin Mulkin 1999, kamar yadda aka gyara.

Ta amince da cewa dan takarar jam’iyya ko wakili da ya lalata ko kwace akwatunan zabe, takardun jefa kuri’a ko kayan zabe kafin lokacin ko bayan zabe ba tare da izinin jami’in zaben da ke kula da wurin zaben ba zai iya fuskantar daurin akalla shekaru 20 ko kuma tara na akalla naira miliyan 40.

Har ila yau, ta amince da shawarar da kwamitin ya bayar na daurin shekaru 15 a gidan yari ga duk wani mutum da ke da hannu a satar akwatin zabe, ba da katin zaben ga mutane ba tare da izini ba, buga rajistar masu jefa kuri’a ba tare da izini ba, buga takardu ba bisa ka’ida ba ko takardun zabe da sauransu.

Kara karanta wannan

N700m na rashawar Diezani: EFCC ta sake gurfanar da Yero tare da sauran

KU KARANTA KUMA: Ina Jin Irin Raɗaɗin da Kuke Ji, Gwamna Ya Lallashi Mutanen Jiharsa

Ta kuma amince da daurin shekaru 10 ga duk mutumin da ya sayar da katin zabe ko kuma yake da duk wani katin jefa kuri’a mai dauke da sunan wani mutum na daban, jaridar Tribune ta ruwaito.

Majalisar ta kuma tanadi hukuncin daurin shekara 15 kan duk jami’in shari’a ko ma’aikacin kotun da ya yi yunkurin sauya sakamakon zabe.

Ta kuma tanadi daurin shekara 15 ko tarar miliyan 30 kan duk jami’in tsaron da ma’aikatan INEC suka yi kokarin yin amfani da shi wajen tafka magudin zabe.

Jerin sunayen kwamishinonin INEC 5 da majalisar dattijai ta tabbatar da su

A wani labarin, mun kawo cewa majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Kwamishinoni biyar a hukumar zaben kasar.

An tattaro cewa majalisar tarayyar ta tabbatar da zabin na Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne bayan nazarin rahoton kwamitinta a kan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, a ranar Talata, 13 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

Har ila yau majalisar ta ki tabbatar da Farfesa Sani Adam daga Arewa ta Tsakiya saboda koke-koken da ake yi a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng