Malami ya amince Inyamurai su sa ido kan shari'ar Nnamdi Kanu, amma da sharadi

Malami ya amince Inyamurai su sa ido kan shari'ar Nnamdi Kanu, amma da sharadi

  • Ministan Shari'a Abubakar Malami ya yabawa Inyamurai bisa kudurin sa ido kan shari'ar Nnamdi Kani
  • A cewarsa, manufarsu mai kyau ce, kuma ba ta saba doka ba, amma akwai sharadi kan hakan
  • A cewarsa, dole a bi doka da oda yayin gudanar da shari'ar, wacce za a yi cikin kwanaki kadan masu zuwa

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN), a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli ya mayar da martani ga matsayar kungiyar koli ta zamantakewar al'adun Ibo, Ohanaeze Ndigbo, na sanya ido kan shari'ar shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Malami, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Umar Gwandu kuma Legit.ng ta gani, ya yi maraba da kafa kungiyar lauyoyin da kungiyar ta yi.

KARANTA WANNAN: ICPC: Da za a dawo da kudaden da su Abacha suka wawura, da Najeriya ta huta da cin bashi

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

Malami ya amince Inyamurai su sa ido kan shari'ar Nnamdi Kanu, amma da sharadi
Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN) | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Malami ya ce bukatar kungiyar kudu maso gabas tana kan tsari

Malami ya ci gaba da cewa shawarar da kungiyar 'yan kabilar Ibo ta yanke ta yi daidai da koyarwar 'yancin sauraren kara wanda ya samo asali daga Sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya.

A kalamansa, cewa ya yi:

"Matsayin kungiyar Ohanaeze Ndigbo a kan lamarin shi ne nuna amincewarsu da kasancewarsu na Najeriya da kuma mika wuya ga bin doka tare da ci gaba da matsayarsu cewa ba sa kyamar shari'ar Nnamdi Kanu."

Ya ce kungiyar:

"Ta nuna wayewa daga irin tunanin kungiyar 'yan asalin yankin Biafra."

Ministan ya tabbatar da cewa shari'ar za ta kunshi abubuwan da doka ta tanada

Malami ya ci gaba da cewa matsayin Ohanaeze Ndigbo kan batun ya dace da tsarin mulki kuma abun a yaba ne.

Ministan ya bayyana fatan cewa tawagar sa ido kan harkokin shari'ar za ta gudanar da ayyukanta da zuciya daya da kuma bin doka a yayin aiwatar da aikinta.

Kara karanta wannan

ICPC: Da za a dawo da kudaden da su Abacha suka wawura, da Najeriya ta huta da cin bashi

KARANTA WANNAN: Aikin Kwangila: Barazanar da Ma’aikatan Banki Ke Fuskanta Na Karancin Albashi

Minista Malami ya caccaki lauyan turai da ya kare Nnamdi Kanu

A wani labarin, Kelechi Amadi ya hadu da fushin Ministan Sharia game da kalamansa kan kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB.

Ministan na kasar Kanada ya sha caccaka daga babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami inda ya yi masa wankin babban bargo, inji rahoton The Cable.

A kwanakin baya ne Madu ya caccaki Minista Malami game da kamun Nnamdi, yana mai cewa idan har da gaske an kama Kanu ba bisa ka'ida ba aka dawo da shi Najeriya, to Malami ya zama abun kunya ga doka da oda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.