Rashin tsaro: Wata jahar Arewa ta dauki Mafarauta 10,000 domin su zama kari ga hukumomin tsaro

Rashin tsaro: Wata jahar Arewa ta dauki Mafarauta 10,000 domin su zama kari ga hukumomin tsaro

  • Gwamnatin Bauchi ta tashi tsaye don tallafawa hukumomin tsaro daga cikin kokarin da take na magance matsalar rashin tsaro a fadin jihar
  • Akalla mafarauta 10,000 aka dauka aiki domin su taimaka wajen yakar 'yan ta'adda, satar mutane, da sauran laifuka
  • Umaru Alkaleri, babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan tsaro, ya bayyana hakan a jihar Bauchi a ranar Lahadi, 11 ga watan Yuli

Kimanin mafarauta 10,000 ne gwamnatin Bauchi ta dauka aiki domin tallafawa kokarin hukumomin tsaro a jihar wajen yaki da rashin tsaro.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Alhaji Umaru Alkaleri, babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin tsaro ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai karin haske game da yanayin tsaro a jihar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya shirya liyafar cin abincin dare tare da sanatoci 109 a yau Talata

Rashin tsaro: Wata jahar Arewa ta dauki Mafarauta 10,000 domin su zama kari ga hukumomin tsaro
Gwamnatin Bauchi ta dauki Mafarauta 10,000 domin su zama kari ga hukumomin tsaro Hoto: AIT News
Asali: UGC

An tattaro cewa jihar ta arewa ta dauki wannan matakin ne a matsayin wani bangare na kudirinta na inganta tsaro a cikin unguwanni da tsare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da ba su ji ba su gani ba.

Kara karanta wannan

Hisbah: An kwamushe wasu mutane da ake zargin suna aikata luwadi a jihar Kano

Alkaleri ya ce an yi rijistar mafarautan ne a duk fadin kananan hukumomi 20 na jihar saboda suna taimakawa a sintiri na yau da kullun da ke fatattakar sansanonin ’yan fashi a cikin daji tare da goyon bayan wasu jami’an tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

Umaru Aliyu wanda shi ne Shugaban kungiyar mafarautan jihar ya ce mambobinsa suna aiki 24/7 ta hanyar yin sintiri a duk wani lungu da sako da ke jihar don ganin 'yan ƙasa sun yi bacci da idanunsu a rufe.

Ya ce kwanan nan, sun kama mutane 29 da ake zargi da satar mutane, fashi da makami da sauran laifuka a jihar kamar yadda suka rusa sansanonin masu satar mutane tsakanin kananan hukumomin Dass da Tafawa Balewa.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro a Najeriya: Wasu 'yan bindiga sun kashe malamin addini a jihar Taraba

Mai taimakawa Gwamnan ya ci gaba da cewa ofishin kungiyar na Inkil kadai yana da ma’aikata 200 a kan aiki 24/7 suna jiran kiraye-kiraye na damuwa daga kowane bangare na garin Bauchi domin a amsa masu cikin gaggawa, ya ce,

Kara karanta wannan

Abokin zamanka shine mutum na farko da zai tabbatar da ko kai mutumin kirki ne - Zahara Buhari

“muna da mafarauta da ke aiki tare da tsaro a dukkanin Kananan Hukumomin 20 na jihar.”

Ba zan bari ’yan bindiga su samu gindin zama a Bauchi ba - Bala Mohammed

A baya mun ji cewa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sha alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta bari miyagun masu aikata laifuka su mamaye jihar tare da hana mutanen jihar damar zuwa gonakinsu ba.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake yaba wa kungiyoyin ’yan banga a cikin jihar kan himmarsu da kuma hadin gwiwar da suke yi da jami'an tsaro domin dakile aikata miyagun laifuka a jihar. Ya ce ba don su ba, da 'yan bindiga sun mamaye jihar, rahoton DN.

Ya fadi hakan ne a lokacin da yake kaddamar da noman rani na bana da kuma sayar da takin zamani a wani bikin da aka gudanar a garin Soro da ke yankin Karamar Hukumar Ganjuwa a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya bayyana matakansa da ya dauka na kare dalibai daga sata a makarantu

Asali: Legit.ng

Online view pixel