Ganduje Ya Dakatar da Kungiyar Masu Bashi Shawari Na Musamman Saboda Rikicin Cikin Gida

Ganduje Ya Dakatar da Kungiyar Masu Bashi Shawari Na Musamman Saboda Rikicin Cikin Gida

  • Ganduje ya dakatar kungiyar manyan mashawarta na musamman saboda wani rikici dake gudana
  • Gwamnatin Ganduje ta ce rikin da ya faru a kungiyar ya dauke hankalin mashawaratan daga aikin da aka daukesu
  • Hakazalika, gwamnatin ta koka kan yadda rashin jituwan z=ya jawo baraka da abun kunya ga gwamnati

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya dakatar da kungiyar manyan mataimaka ta musamman a Kano saboda rikicin shugabanci, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya ce gwammnati ta lura cewa abubuwan dake gudana a kungiyar suna dauke musu hankali daga asalin ayyukansu da kuma ba da gudunmawarsu ga gwamnati.

Ya ce rashin jituwar da ke tsakanin shugabannin biyu na kungiyar ya haifar da rashin jin dadi da kunya ga gwamnati wanda in ba a kula ba, za ta iya lalata manufofi da burin da aka sanya kan SSA din.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Kajuru tare da iyalansa 13

KARANTA WANNAN: Murna: Hotunan Atiku da Daya Daga Cikin 'Yan Matan Chibok Lokacin da Ta Kammala Digiri

Ganduje ya ruguza kungiyar SSA ta 'yan siyasa a fadin jihar Kano
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Depositphotos

Sanarwar ta ce:

“Akwai bukatar a ci gaba da zama cikin lumana tsakanin Manyan Mataimaka na Musamman. A kan wannan ne Mai Martaba, Gwamnan Jihar Kano, ya bayar da umarnin a dakatar da taron kungiyar ta SSA tare da jagororinta guda biyu don haka, aka dakatar dasu a yanzu.
"Don haka an umarci dukkan Manyan Mataimaka na Musamman da su maida hankali tare da yin aiki daidai da jadawalin ayyukansu na ci gaban gwamnati."

Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ganduje Ya Taka Hoton Kwankwaso

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa taka hoton kwankwaso da gwamna Ganduje yayi ba dagangan bane kuma ba shiryayyen abu bane, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, shine ya faɗi haka, yace hoton da ake yaɗawa na gwamna Ganduje yana taka Fastar kwankwaso a wajen taron APC da ya gudana ranar Asabar, amma ba da sanin mai girma gwamna hakan ta faru ba.

Kara karanta wannan

Murna: Hotunan Atiku da Daya Daga Cikin 'Yan Matan Chibok Lokacin da Ta Kammala Digiri

Kwamishinan ya ƙara da cewa kowane irin banbancin siyasa ke tsakanin mutanen biyu, ba halayyar gwamna Ganduje bane yayi irin wannan abun ga wani ɗan siyasa, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: NDLEA Ta Cafke Dillalan Kwayoyi 89 da Tan 2,800 Na Haramtattun Magunguna a Kebbi

Gwamnatin El-Rufa'i Ta Garkame Bankin Fidelity a Kaduna Saboda Kudin Haraji

A wani labarin, Hukumar tattara haraji ta jihar Kaduna (KADIRS), a ranar Alhamis ta garkame rassa hudu na Bankin Fidelity saboda kin biyan sama da Naira miliyan 43.3 na haraji, Daily Nigerian ta ruwaito.

Rassan da aka garkame sun hada da na titin Ali Akilu, Ahmadu Bello Way, hanyar Polytechnic kan mahadar Maimuna Gwarzo, da kuma hanyar Kachia, duk a cikin garin Kaduna.

Ms Aisha Mohammed, mai ba da shawara kan harkokin shari'a kuma sakatariyar hukumar KADIRS, ta shaida wa manema labarai bayan garkamewar a Kaduna, cewa an garkame rassan ne saboda zargin kin biyan kudaden haraji na Naira miliyan 43.3 daga shekarar 2011 zuwa 2020.

Kara karanta wannan

Allah Ya kunyata Abduljabbar tun a duniya - Mallam Muhammad Rijiyar Lemo

Asali: Legit.ng

Online view pixel