Aikin Kwangila: Barazanar da Ma’aikatan Banki Ke Fuskanta Na Karancin Albashi
Tsokacin Edita: Aikin banki na daya cikin ayyukan da ke bukatar mayar da hankali, musamman duba da yadda aikin ke ta'ammuli da dukiyar al'umma da kuma amanarsu. Wannan yasa, lamari ne mai bukatar lissafi da jarircewa da kuma rikon amana.
Abu ne sananne ka ga ma'aikacin banki ya wuni a wurin aiki, duk da irin sammako da ake yi. Hirar AlJazeera da Legit.ng Hausa ta samo ta bayyana irin azabar da ma'aikatan banki ke sha, da kuma karancin samu karin girma da karin albashi da suke fuskanta, musamman masu aikin kwangila.
Aiki a bankunan kasuwanci a Najeriya ya kasance aiki mai matukar cike takaici, kamar yadda wani matashi mai suna Basit ya koka kan yanayin aikin da yake a banki.
Matashin mai shekaru 28, wanda aka sakaya sunansa don kare bayanansa, yana aiki a matsayin jami'in bayar da kudi a bankin Fidelity a Najeriya tun shekarar 2015.
Shekaru shida, yana reshen Fidelity, yana aiki a matsayin da aka dauke shi, da karamin albashin Naira 68,000 ($ 165) a wata ba tare da karin girma ba.
Ba ka'ida ne aikin Basit ya rasa ba, tsarin da yake aiki a karkashinsa ne matsalar. A rubuce shi ba cikakken ma'aikaci bane.
KARANTA WANNAN: Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17000 a sansani a jihar Borno
Duk tsawon lokacin da ya yi yana aiki a wurin, ya kasance ma’aikacin kwangila da wata hukumar daukar ma’aikata ta dauka aiki wacce bai taba hulda da ita kai tsaye ba.
Kasancewarsa dan kwangila yana nufin Basit bashi da wata hanyar samun ci gaban aiki a banki, ko fa'idodi kamar inshora, fansho, ko kuma tagomashin sallama idan zai bar aiki.
Idan bankin Fidelity suka gaji da aiki dashi, ko kuma kawai suna son rage kashe kudade, za su iya korarsa idan kwantiraginsa ta zo sabuntawa duk bayan shekaru biyu.
A halin yanzu, hukumar da ta samar masa aiki tana karbe wani kaso daga cikin kudinsa a kowane wata a matsayin "kwamisho".
Bankin Fidelity bai amsa bukatar jaridar Al-Jazeera ba don jin ta bakin ta. Amma labarin Basit lallai gaskiya ne kuma na musamman.
Fiye da 42% na ma’aikatan banki a Najeriya ma’aikatan kwangila ne har zuwa zango na uku a bara, in ji Ofishin Kididdiga na Kasa. Ragowar kuma ma'aikata ne na cikakken tsari tare da bankuna - kusan kashi baya bisa uku daga cikinsu manyan ma'aikata ne.
Ko da yake 'yan kungiyar kwadagon da jami'an gwamnati sun ce ana magance matsalolin da suka dabaibaye ma'aikatan bankin kwangilar, amma an samu jinkirin kawo mafita.
Kuma har sai sun yi kafin a samu zabin aiki a bangaren banki galibin ma'aikatan kwantaragin matasa ake dauka masu jini a jika.
Ana kunu dan riba
Basit sau da yawa yakan yi tunanin barin aikinsa na banki. Amma yiyuwar a dama dashi a wani fannin abu ne mai matukar wahala a Afrika saboda karancin aikin yi.
Adadin rashin aikin yi a hukumance ya karu zuwa 33.3% a cikin watanni ukun karshe na shekarar da ta gabata - mafi girma a tarihi kuma daga cikin mafi girma a duniya.
Fiye da rabin yawan ma'aikata kusan miliyan 70 na kasar sun kasance ba su da aikin yi a karshen shekarar bara ta 2020 ko kuma ba sa aiki na cikakken tsari.
Wannan karancin ayyukan yi ya sanya shi zama kasuwa mai riba ga masu daukar ayyuka, wanda ya kai ga ma’aikata kusan ba su da ikon tattaunawa don tsadance jingarsu - balle bayyana bukatarsu ko jin dadin aiki da zabi.
A bangaren Basit, wannan na nufin azabtarwa ta awanni 10 da ya kai ga karancin lokacin da zai iya tunanin sauyin aiki ko neman wani.
A cewarsa:
‘’Kalubalen shi ne da kyar za ka samu lokacin da za ka je neman aiki a wani wuri. za ka bar gida tun da karfe 5 ko 6 na safe kuma ka dawo da miasalin karfe 6 na yamma ko makamancin haka.
"Ta yaya zan dawo cikin gajiya kamar wannan kuma har na fara neman wani aiki yayin da na san cewa ba lallai na sam ba? ''
Aikin kwangila ya kasance silar kasuwar kwadago ta Najeriya shekaru da yawa, amma ta fi yawa musamman a bankuna da kuma fannin man fetur.
KARANTA WANNAN: Ganduje Ya Dakatar da Kungiyar Masu Bashi Shawari Na Musamman Saboda Rikicin Cikin Gida
Gwamnatin El-Rufa'i Ta Garkame Bankin Fidelity a Kaduna Saboda Kudin Haraji
A wani labarin, Hukumar tattara haraji ta jihar Kaduna (KADIRS), a ranar Alhamis ta garkame rassa hudu na Bankin Fidelity saboda kin biyan sama da Naira miliyan 43.3 na haraji, Daily Nigerian ta ruwaito.
Rassan da aka garkame sun hada da na titin Ali Akilu, Ahmadu Bello Way, hanyar Polytechnic kan mahadar Maimuna Gwarzo, da kuma hanyar Kachia, duk a cikin garin Kaduna.
Ms Aisha Mohammed, mai ba da shawara kan harkokin shari'a kuma sakatariyar hukumar KADIRS, ta shaida wa manema labarai bayan garkamewar a Kaduna, cewa an garkame rassan ne saboda zargin kin biyan kudaden haraji na Naira miliyan 43.3 daga shekarar 2011 zuwa 2020.
Asali: Legit.ng