Rikici: Mataimakin gwamna na kokarin karbe kujerar Matawalle, PDP ta yi martani

Rikici: Mataimakin gwamna na kokarin karbe kujerar Matawalle, PDP ta yi martani

  • PDP ta bayyana goyon bayan ta kan cewa, a yanzu, Mahdi Aliyu Gusau shine gwamnan jihar Zamfara
  • A baya gwamnan jihar Zamafa Matawalle ya koma APC, lamarin da ya jawo PDP ta ce kujerarsa dai kam ya rasa ta
  • Biyo bayan hana Gusau shiga ofishinsa a matsayin gwamnan jihar ta Zamfara, PDP ta yi Allah wadai da hakan

An rahoto cewa Mahdi Aliyu Gusau, mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya samu goyon bayan jam’iyyar PDP don karbar kujerar Bello Matawalle a matsayin gwamnan jihar dake a arewa maso yamma.

Wannan ya biyo bayan sauya shekar da Gwamna Matawalle ya yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki tare da sauran zababbun masu rike da mukaman siyasa a jihar.

Sai dai, Gusau ya tsaya, yana mai cewa ba a zabe shi don ya fice daga PDP zuwa wata jam'iyyar ba, jaridar The Nation ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17000 a sansani a jihar Borno

Read also

Shugabancin Kasa: Yeriman Bakura ya magantu kan tsayawa takara a 2023 karkashin APC

PDP ta shirya karbe kujerar gwamna Matawalle, za ta goyi bayan Mahdi
Mahdi Aliyu Gusau, mataimakin gwamnan jihar Zamfara | Hoto: naijanews.com
Source: UGC

Mataimakin gwamnan ya yi hasashen matakin da zai dauka na tsige Matawalle a kan hukuncin Kotun Koli na 2019 wanda ya soke nasarar da dukkan ‘yan takarar APC suka yi a zaben.

Amma, an tattara cewa, rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara na toshe yunkurin Gusau na karbar mukaminsa na gwamna, lamarin da ya haifar da martani daga PDP a ranar Lahadi, 11 ga watan Yuli.

PDP ta yi Allah wadai da hana Gusau shiga ofis

Da yake magana kan lamarin kakakin PDP Kola Ologbondiyan ya yi Allah wadai da abinda ya kira da yunkurin da 'yan sanda ke yi na gurbata ikon da doka ta ba mataimakin gwamnan.

Jam’iyyar adawar ta yi ikirarin cewa Matawalle ya rasa kujerarsa ne a ranar da ya sauya sheka zuwa APC tare da gargadin ‘yan sanda game da muzgunawa ga mataimakin gwamnan da ake yi.

Ta kuma yi Allah wadai da hukumomin ‘yan sanda a Zamfara kan “haramtacciyar doka da nuna fushin” hana wani taron gangami da mataimakin gwamnan ya shirya.

Read also

Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17,000 a sansaninsu na jihar Borno

Jam’iyyar ta PDP ta ce mataimakin gwamnan na da ikon da doka ta ba shi damar hawa kujerar gwamnan “a halin da gwamnan ya bar ofishinsa”, daidai da hukuncin da Kotun Koli ta yanke.

A cewar jam'iyyar, ya kamata 'yan sanda su bai wa mataimakin gwamnan "dukkan kariya da gata" maimakon "muzguna mishi", jaridar The Guardian ma ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: Kaduna: Sojoji sun bazama daji don ceto sarkin Kajuru da iyalansa daga 'yan bindiga

Shugabancin Kasa: Yeriman Bakura ya magantu kan tsayawa takara a 2023 karkashin APC

A wani labarin, Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmed Yerima, ya ce zai janye takararsa ta kujerar shugaban kasa a 2023 idan har jam'iyyar APC mai mulki ta ba da tikitin zuwa yankin Kudu.

Yerima ya tattara hankalinsa gefe kan babban zaben shekarar 2023 yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Lahadi, Punch ta ruwaito.

Read also

Yanzu-Yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan Kaduna, Bala Bantex, ya mutu

Yerima ya ce bai ga dalilin da zai sa ya fice daga takarar ba, duk da kiran da gwamnonin kudu suka yi a taron su na karshe a Legas.

Source: Legit.ng News

Online view pixel