Yanzu-Yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan Kaduna, Bala Bantex, ya mutu

Yanzu-Yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan Kaduna, Bala Bantex, ya mutu

  • Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kaduna Architect Barnabas Bala Bantex ya riga mu gidan gaskiya
  • Bala Bantex ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin tarayya Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya
  • Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya tabbatar da rasuwar Bantex, ya kuma bada hutun kwana daya don zaman makoki

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Architect Bala Bantex, ya rasu yana da shekaru 64 a duniya, Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyoyi daga gidan gwamnatin jihar Kano sun tabbatarwa Daily Nigerian rahoton.

DUBA WANNAN: Sarki mai daraja ta ɗaya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki

Yanzu-Yanzu: Tsohon mataimakin gwamnan Kaduna, Bala Bantex, ya mutu
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Bala Bantex. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Mr Bantex ya yi aiki a matsayin mataimakin gwamna ga Gwamna Nasir El-Rufai daga shekarar 2015 zuwa 2019 a lokacin da ya yi murabus domin yin takarar kujerar sanata amma bai yi nasara ba.

Architect Barnabas Bantex, wanda ya rike mukamin mataimakin gwamna a jihar Kaduna daga Mayun 2015 zuwa Mayun 2019, ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi a Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya bada hutun kwana ɗaya a Kaduna domin zaman makokin Bantex

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa Bantex ya yi aiki a wurare da dama a Kaduna kafin ya zama matsayin gwamna ciki har da wakili a taron yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima da aka yi a 1994.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Shahararren mawaƙin Nigeria, Sound Sultan ya mutu

Gwamna El-Rufai ya bada hutun kwana daya don zaman mokokin Bantex

A wani labarin daban, Gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana ranar Litinin 12 ga watan Yulin 2021 a matsayin ranar hutu domin karrama ayyukan tsohon mataimakin gwamna, Barnabas Yusuf Bala Bantex, wanda ya rasu a safiyar ranar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Sanarwar da gwamnan ya fitar da bakin mashawarcinsa na musamman kan kafafen watsa labarai, Muyiwa Adekeye, ta ce Malam Nasir El-Rufai ya aike da sakon ta'aziyya na musamman ga iyalan Bantex.

A cewar sanarwar, Gwamna El-Rufai ya ce ya gode wa Allah bisa bashi baiwan sani da aiki tare da Bantex.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: El-Rufa'i Ya Tabbatar da Mutuwar Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna

Ya kuma jadada jajircewar da marigayin ya yi wurin ganin an samu cigaba da jihar Kaduna sannan ya yi addu'ar Allah ya jikansa ya kuma bawa iyalansa hakurin jure rashinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel