Da Ɗumi-Ɗumi: El-Rufa'i Ya Tabbatar da Mutuwar Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna
- Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya tabbatar da mutuwar tsohon mataimakinsa , Bantex
- Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin ɗan uwansa kuma abokin gwagwarmaya
- Yace gwamnati da jama'ar jihar Kaduna za su yi matuƙar kewarsa, saboda ƙoƙarinsa na kawo cigaba
Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya tabbatar da mutuwa tsohon mataimakin gwmanan jihar, Barbanas Bala Bantex, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Bayan Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Kajuru, Shugaban Majalisa Ya Yi Zazzafan Martani
El-Rufa'i ya bayyana cewa a wurinshi ya rasa babban aboki kuma abokin aiki a wajen kawo cigaban jihar Kaduna.
Gwamnan, a wani jawabi ɗauke da sanya hannunsa, yace yana cikin wani yanayi mai wahala yayin da ya samu labarin mutuwar abokinsa kuma ɗan uwansa, Barnabasa Yusuf Bala (Bantex).
Gwamnan Yace: "Tun sanda muke karatun jami'a a shekarar 1970 zuwa sanda muka zama abokan aiki a gwamnatance, Bantex ya kasance mai dogaro da kanshi kuma mutum ne mai basira sosai."
"Tare da shi muka yi gwagwarmayar kawo canji a jihar Kaduna a 2015. A zangon mulkin mu na farko yayi amfani da dukkan basirar sa wajen kawo cigaba a Kaduna lokacin yana mataimakin gwamna."
Kaduna za ta yi kewar Bantex
Malam El-Rufa'i ya ƙara da cewa marigayin ya yi aiki da dama don kawo cigaba a Kaduna tun kafin ya zama mataimakin gwamna bayan zaɓen 2015.
Yace marigayin ya riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Ƙaura, sannan ya shiga majalisar dokokin jihar Kaduna a matsayin mai wakiltar ƙaramar hukumar ƙaura, kamar yadda the nation ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Illar COVID19: Yadda Magidanta a Najeriya Ke Fama da Hauhawar Farashin Kayan Abinci, Duk da Ƙarancin Kuɗin Shiga
Yace: "Zamu yi kewarsa sosai, basirarsa da ƙoƙarinsa wajen kawo cigaba a Kaduna."
"Na yi magana da iyalansa, kuma na musu ta'aziyya a madadin gwamnatin Kaduna da al'ummar jihar baki ɗaya."
"Zamu yi aiki tare da iyalansa wajen ganin mun yi bankwana da mutumin da ya ke tunanin mu har a lokacin da ba shi da lafiya."
A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Yi Martani Kan Harin Zamfara da Kaduna, Ya Umarci Dakarun Soji Su Murkushe Yan Ta'adda
Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hare-hare da aka kai kwanan nan jihar Zamfara da Kaduna.
Shugaban ya umarci sojoji da su ɗauki matakin murkushe duk wasu yan ta'adda ta yaren da zasu fahimta.
Asali: Legit.ng