El-Rufai ya bada hutun kwana ɗaya a Kaduna domin zaman makokin Bantex

El-Rufai ya bada hutun kwana ɗaya a Kaduna domin zaman makokin Bantex

  • Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bada hutun ranar Litinin domin karrama marigayi Bala Bantex
  • Marigayi Architect Yahaya Bala Barnabas Bantex ne yi yi aiki a matsayin mataimakin Gwamna El-Rufai daga 2015 zuwa 2019
  • Yahaya Bala Barnabas Bantex ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja baya gajeruwar rashin lafiya

Gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana ranar Litinin 12 ga watan Yulin 2021 a matsayin ranar hutu domin karrama ayyukan tsohon mataimakin gwamna, Barnabas Yusuf Bala Bantex, wanda ya rasu a safiyar ranar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

El-Rufai ya bada hutun kwana daya a Kaduna domin zaman makokin Bantex
El-Rufai ya bada hutun kwana daya a Kaduna domin zaman makokin Bantex. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sarki mai daraja ta ɗaya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki

Sanarwar da gwamnan ya fitar da bakin mashawarcinsa na musamman kan kafafen watsa labarai, Muyiwa Adekeye, ta ce Malam Nasir El-Rufai ya aike da sakon ta'aziyya na musamman ga iyalan Bantex, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: El-Rufa'i Ya Tabbatar da Mutuwar Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna

Architect Barnabas Bantex, wanda ya rike mukamin mataimakin gwamna a jihar Kaduna daga Mayun 2015 zuwa Mayun 2019, ya rasu ne a ranar Lahadi a Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

A cewar sanarwar, Gwamna El-Rufai ya ce ya gode wa Allah bisa bashi baiwan sani da aiki tare da Bantex.

KU KARANTA: Ka Yafe Wa Igbobo, Ya Wahala, Ya Gane Kurensa: Basaraken Yarbawa Ya Roƙi Buhari

Ya kuma jadada jajircewar da marigayin ya yi wurin ganin an samu cigaba da jihar Kaduna sannan ya yi addu'ar Allah ya jikansa ya kuma bawa iyalansa hakurin jure rashinsa.

Jihar Kaduna za ta yi kewar Bala Bantex

Gwamna El-Rufa'i ya ƙara da cewa marigayin ya yi aiki da dama don kawo cigaba a Kaduna tun kafin ya zama mataimakin gwamna bayan zaɓen 2015.

Yace marigayin ya riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Ƙaura, sannan ya shiga majalisar dokokin jihar Kaduna a matsayin mai wakiltar ƙaramar hukumar ƙaura, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Kajuru, Shugaban Majalisa Ya Yi Zazzafan Martani

Shahararren mawaƙin Nigeria, Sound Sultan ya mutu

A wani labarin daban, Olanrewaju Fasasi, tauraron mawaƙin Nigeria, da aka fi sani da Sound Sultan ya riga mu gidan gaskiya, Daily Trust ta ruwaito.

A cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi, iyalan mawakin sun ce ana masa maganin cutar kansa na moƙogoro ne kafin rasuwarsa.

The Punch ta ruwaito an fara yi wa mawaƙin maganin kansa ta Chemotherapy ne tun a watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel