Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Yan Bindiga da dama, Ta Ƙwato Manyan Makamai a Hannunsu

Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Yan Bindiga da dama, Ta Ƙwato Manyan Makamai a Hannunsu

  • Jami'an yan sanda sun samu nasarar damƙe tawagar wasu masu garkuwa da mutane a jihar Abia
  • Jami'an sun kwato makamai da da dama a hannun su, waɗanda suka hada bindiga kirar AK-47 da alburusai
  • Wata majiya daga hukumar yan sanda ta tabbatar da lamarin, tace ana cigaba da bincike

Rundunar operation ITR ta hukumar yan sanda ta yi ram da wasu yan bindiga 6 da ake zargin masu garkuwa ne a wurare daban-daban a jihar Abia, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: Shugaba Buhari Ya Soke Taron Majalisar Zartarwa FEC

Jami'an yan sandan sun samu nasarar ƙwato bindigar AK-47, da kuma alburusanta guda 25, da kuma wata mota da tawagar yan ta'addan ke amfani da ita.

Wata majiya daga cikin jami'an yan sanda ta shaida wa manema labarai cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu.

Kuma sun bayyana irin ta'asar da suka yi, daga ciki harda sace Mr Aniebue Onyebuchi, da sauran su a faɗin jihar Abia.

Yan sanda sun damƙe masu garkuwa
Rundunar Yan Sanda Ta Cafke Yan Bindiga da dama, Ta Ƙwato Manyan Makamai a Hannunsu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Daga cikin waɗanda dubun su ta cika akwai shugaban tawagar, Chibuike Iheoma, da kuma mataimakinsa, Samuel Udochukwu.

Sauran sun haɗa da, Udo Onwukwe, wanda shine mai leƙen asiri kuma shine mamallakin ginin da suke aje wanda suka yi garkuwa da shi. Sai kuma mai gadin wanda aka sace, Okechukwu Obioma.

Sauran mambobin sun haɗa da Emeka Okedum da Saviour Akpan, waɗanda sune direbobin tawagar.

KARANTA ANAN: Sojoji Sun Gudanar da Addu'ar Kwana 40 Ga Marigayi COAS Ibrahim Attahiru

Hukumar yan sanda bata tabbatar ba a hukumance

Da aka tuntuɓi kakakin hukumar yan sandan Abia, SP Geoffrey Ogbonna, ta wayar salula, bai ɗaga kiran ba.

Amma wani babban jami'i a hukumar yan sanda, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da kama mutanen.

Yace: "Eh an kama wasu masu garkuwa, amma a halin yanzun ana kan gudanar da bincike domin kamo waɗanda suka tsere."

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Taya Matawalle Murna, Ya Faɗi Dalilin Gwamnan Na Sauya Sheƙa Zuwa APC

Shugaba Buhari ya aike da saƙon murna ga gwamna Matawalle bisa sauya shekar da yayi zuwa APC, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Buhari ya bayyana cewa matakin da gwamnan ya ɗauka yana da nasaba da kyakkyawan jagorancin da APC ke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel