Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Soke Taron Majalisar Zartarwa FEC

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Soke Taron Majalisar Zartarwa FEC

  • Shugaba Buhari ya soke taron majalisar zartarwa da aka saba gudanarwa duk ranar Laraban mako
  • Har yanzun babu wani cikakken dalilin soke taron a hukumance daga fadar shugabam ƙasa
  • Taro na ƙarshe da yan majalisar zartarwa suka gudanar shine na makon da ya gaba ranar Laraba 23 ga watan Yuni

An soke taron majalisar zartarwa (FEC), wanda shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ke jagoranta, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Rundunar Soji Ta Gudanar da Addu'ar Kwana 40 Ga Marigayi COAS Ibrahim Attahiru

Har yanzun babu wani dalili a hukumance da yasa aka soke zaman taron na majalisar zartarwa wanda ya kamata a gudanar yau Laraba 30 ga watan Yuni.

Taron FEC na karshe shine wanda ya gudana makon da ya gabata, ranar Laraba 23 ga watan Yuni a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.

Shugaban Ƙasa Buhari
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Soke Taron Majalisar Zartarwa FEC Hoto: @MuhammaduBuhari
Asali: Instagram

An gabatar da taron ta hanyar amfani da fasahar zamani (Virtually) kuma ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da, Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da kuma shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: FG Ta Faɗi Ranar da Zata Kulle Layukan Wayar da Ba'a Haɗasu da NIN Ba

Sauran sun haɗa da, ministan shari'a, Abubakar Malami, ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu da ministan birnin tarayya, Mohammed Bello.

A wani labarin kuma Wata Sabuwa, Obasanjo Ya Sake Yin Magana a Kan Jita-Jitar An Sauya Buhari da Jibrin Sudan

Obasanjo ya sake maganan kan jita-jitar da aka yi a baya lokacin da Buhari ya daɗe a Landan neman Lafiya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Tsohon shugaban yace wannan rahoton da aka yaɗa a wancan lokacin babban abun dariya ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel