Shugaba Buhari Ya Taya Matawalle Murna, Ya Faɗi Dalilin Gwamnan Na Sauya Sheƙa Zuwa APC
- Shugaba Buhari ya aike da saƙon murna ga gwamna Matawalle bisa sauya shekar da yayi zuwa APC
- Buhari ya bayyana cewa matakin da gwamnan ya ɗauka yana da nasaba da kyakkyawan jagorancin da APC ke yi
- Ya kuma roƙi jiga-jigan APC da su cigaba da aiki tare domin tabbatar da nasarar jam'iyyar har bayan 2023
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya taya gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, murnar sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC, kamar yadda premium times ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Abun Mamaki: Wani Fursuna Ya Yi Digirin Digirgir a Fannin Sadarwa a Gidan Yari
Buhari ya bayyana cewa gwamnan ya ɗauki matakin sauya sheƙa zuwa APC ne bayan ya gano cewa jam'iyyar na ƙara ƙarfi saboda kyakkyawan jagorancinta, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
A wani saƙo da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya isar a madadin shugaban ƙasa a wurin taron tarbar gwamna Matawalle a Gusau, Shugaba Buhari yace:
"Ina alfahari da matakin da ka ɗauka na sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki a lokacin da ya dace, kuma kofar mu a buɗe take ga duk wani ɗan siyasa da ya gano kudirin mu na gina Najeriya."
"Matakin da ka ɗauka na komawa jam'iyya mai mulki ya tabbatar da cewa kudirorin mu da kyakkyawan shugabancin mu na daga cikin dalilin da yasa yan Najeriya ke ƙaunar APC."
Buhari ya roƙi jiga-jigan APC su cigaba da aiki tare
Shugaba Buhari yayi amfani da taron wajen jawo hankalin gwamnonin APC da kuma zaɓaɓɓun yan majalisu da su cigaba da aiki tuƙuru don tabbatar da jam'iyyar ta riƙe girmanta, ta sake lashe zaɓen 2023 dake tafe.
Buhari ya tuna wa zaɓaɓɓun yan jam'iyyar da cewa "aikin da kuka yi a kowane mataki shine zai yi tasiri a kan goben jam'iyyar."
KARANTA ANAN: Jigon PDP Ya Caccaki El-Rufa'i, Ya Buƙaci Ya Sadaukar da Albashinsa Ga Ɗalibai
Ya ƙara da cewa ya kamata shugabannin APC su gujewa duk wani abu da ka iya zuwa ya dawo domin ƙara gina jam'iyyar ta ƙara ƙarfi.
A wani labarin kuma Dalilin da Yasa Na Gudu, Nnamdi Kanu Yayi Jawabi a Gaban Kotu
Shugaban ƙungiyar tawaren IPOB da aka kama ya yi magana a gaban kotu, ya faɗi dalilin da yasa ya fice daga Najeriya.
A shekarar 2017 alkalin babbar kotun tarayya dake Abuja, Binta Nyako, ta bada belin Kanu bisa sharuɗɗa masu tsauri.
Asali: Legit.ng