Da Duminsa: An saki sakamakon jarrabawar JAMB, duba yadda zaka iya ganin sakamakon ka a wayar salularka

Da Duminsa: An saki sakamakon jarrabawar JAMB, duba yadda zaka iya ganin sakamakon ka a wayar salularka

  • Hukumar shirya jarrabawar shiga makaratun gaba da sakandare, JAMB, ta fitar da sakamakon jarrabawar bana
  • Hukumar ta ce duk wani dalibi da ya rubuta jarrabawar yana iya duba sakamakonsa ta hanyar amfani da wayar salularsa
  • Har wa yau, hukumar ta ce akwai sakamakon wasu dalibai kalilan da bata saki ba don ana bincike a kansu

Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare, JAMB, ta fitar da sakamakon dalibai da suka zana jarrabawar UMTE na 2021 a cibiyoyin CBT 720 daga ranar Asabar 19 zuwa 22 ga watan Yunin 2021, Daily Trust ta ruwaito.

Amma hukumar ta rike sakamakon wasu tsirarun dalibai 'domin yin bincike a kansu' a cewar shugaban sashin tsare-tsare da hulda da jama'a na hukumar, Fabian Benjamin.

Dalibai na rubuta jarrabawar JAMB
Dalibai na rubuta jarrabawar JAMB. Hoto: Daily Trust
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Dakatar da Twitter ya hana wa gwamnonin PDP kafar yaɗa labaran ƙarya, Fadar Shugaban ƙasa

Benjamin, wanda ya ce hukumar ba za ta yi wata-wata ba wurin janye sakamakon duk wani dalibi da aka gano ya yi magudin jarrabawa, yana mai cewa za a fitar da sauran sakamakon nan gaba kamar yadda Guardian ta ruwaito.

Yadda za ka duba sakamakon jarrabawar da wayarka

Ya shawarci dalibai su duba sakamakon jarrabawarsu ta hanyar aike sakon kar ta kwana daga wayarsu kamar haka, UMTERESULT zuwa ga 55019 da lambar da aka yi amfani da ita wurin yin rajistan JAMB din.

KU KARANTA: An fara amfani da 'tsafi' domin hana ƴan bindiga kai wa ƴan sanda hari a kudu maso gabas

Ya ce:

"Hukumar ta gamsu da cewa amfani da lambar dan kasa wato NIN wurin yin rajistar jarrabawar ya taimaka wurin rage magudin zabe a UMTE 2021 yana mai cewa jarabawar ta bana ce aka samu karancin magudin zabe tun fara jarrabawar na CBT a Nigeria."

Sai dai ya kara da cewa hukumar za ta yi bitar faifan bidiyo na CCTV da ta nada yayin jarrabawar da wasu kayayyakin zamani domin gano wadanda suka yi magudin jarrabawar.

Kimanin mutane miliyan 1.3 ne suka yi rajistar jarrabawar a bana.

A wani labarin daban, wani mutum mai shekaru 40, Sani Abubakar, a ranar Alhamis, ya yi ƙarar ƙaninsa Adda'u Ahmed gaban kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa, kan zargin ƙin ƙiyayya ga wasiyyar mahaifinsu, Vanguard ta ruwaito.

Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ya kuma yi ƙarar wani Malam Shuaibu.

Ya shaidawa kotu cewa mahaifinsu da Allah ya yi wa rasuwa ya bar wasiyya cewa a mayar da ɗaya daga ɗakunan gidan zuwa masallaci amma wadanda ya yi ƙarar sun saɓa umurnin mahaifin a cewar rahoton na Vanguard.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel