Dakatar da Twitter ya hana wa gwamnonin PDP kafar yaɗa labaran ƙarya, Fadar Shugaban ƙasa
- Fadar shugaban kasa ta mayarwa gwamnonin jam'iyyar PDP martani kan batun dakatar da shafin Twitter a Nigeria da FG ta yi
- Gwamnonin na jam'iyyar hamayya ta PDP sun soki dakatarwar suna mai cewa hana ƴan Nigeria ƴancin bayyana ra'ayinsu ne
- Sai dai fadar shugaban ƙasa ta ce gwamnonin na PDP suna fushi ne don sun rasa kafar da suka amfani da ita wurin yaɗa labaran ƙarya
Fadar shugaban ƙasa ta ce gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, suna bakin ciki kan dakatar da Twitter ne saboda ya rage damar da suke da shi na yaɗa 'labaran ƙarya', rahoton The Cable.
A ranar 4 ga watan Yuni, gwamnatin tarayya ta dakatar da shafin dandalin sada zumuntan kan ikirarin cewa ana amfani da shi wurin raba kan ƴan ƙasa.
DUBA WANNAN: An kama matar da ta damfari ɗan siyasa N2.6m da sunan za a yi amfani da 'iskokai' a taimaka masa ya ci zaɓe
A martanin ta kan dakatarwar, kungiyar gwamnonin PDP cikin sakon da ta fitar ta soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan dakatar da Twitter a Nigeria.
A bangarensa, mai magana da yawun shugaban ƙasa Garba Shehu, a martanin da ya yi ranar Laraba ya ce sanarwa da kungiyar gwamnonin PDP ya fitar ya nuna wa ƴan Nigeria, 'abin da yasa bai kamata a mika wa jam'iyyar da wakilanta mulki a ƙasa ba', kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.
"Jam'iyyar PDP na kokawa kan dakatar da Twitter da gwamnatin tarayya ta yi - don hakan ya rage damar da suke da shi na yaɗa labaran bogi da ƙirƙirar labarai da ba za su amfani Nigeria da mutanen kasar ba," in ji Shehu.
Ya ƙara da cewa gwamnonin na PDP sun bada shawarar kan yadda za a magance ƙallubalen da kasar ke fuskanta na annobar korona da tabarbarewar tattalin arziki a duniya, sai dai neman a ƙara musu kudi tare da raki kan rashin damar zuwa dandalin sada zumunta domin su yaɗa ƙarya da ƙiyayya.
A wani rahoton daban kun ji cewa Yinusa Ahmed, dan majalisar wakilai na kasa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce an fara ganin alherin dakatar da shafin sada zumunta na Twitter da gwamnatin Nigeria ta yi, The Cable ta ruwaito.
Within Nigeria ta ruwaito cewa ya ce abubuwan da yan Nigeria ke yi a dandalin na haifar da rigingimu ne a kasa amma yanzu kura ta fara lafawa sakamakon dakatarwar da gwamnati ta yi.
Ahmed ya yi wannan jawabin ne yayin hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng