Harin makarantar Kebbi abun damuwa ne, barazana ne ga tsaro a arewa maso yamma – El-rufai

Harin makarantar Kebbi abun damuwa ne, barazana ne ga tsaro a arewa maso yamma – El-rufai

  • Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi Allah wadai da sace dalibai da yan bindiga suka yi a makarantar Kebbi
  • El-Rufai ya ce hakan abun damuwa ne sosai domin yana nuna hatsarin da yankin arewa maso yamma ke ciki ta bangaren tsaro
  • Ya ce rashin tsaro da ke addabar jihar Kebbi a yanzu zai yi mummunan tasiri ga noman abinci

Nasir el-Rufai, gwamnan Kaduna, ya ce sace yara ‘yan makaranta da aka yi kwanan nan a Kebbi ba alama mai kyau ba ne ga lamarin tsaro a arewa maso yamma.

El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kaiwa Atiku Bagudu, gwamnan Kebbi, a ranar Alhamis, jaridar The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Marigayi kwamishinan Ebonyi ya farka daga mutuwar da yayi? Gwamna Umahi ya magantu

Harin makarantar Kebbi abun damuwa ne, barazana ne ga tsaro a arewa maso yamma – El-rufai
Gwamna Nasir El-Rufai ya ce harin da 'yan bindiga suka kai makarantar Kebbi barazana ne ga tsaro a arewa maso yamma Hoto: The Cable
Asali: UGC

A ranar 17 ga watan Yuni, wasu ‘yan bindiga sun kai hari Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri, Kebbi, suka yi awon gaba da dalibai da malamai da dama.

Kawo yanzu, jami'an tsaro sun kubutar da mutane 11 daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.

Da yake magana a Kebbi, el-Rufai ya nuna bakin ciki kan harin, sannan ya yi kira da a dauki matakan gaggawa don magance matsalar rashin tsaro a yankin.

Gwamnan ya bayyana cewa rashin tsaro da ke addabar jihar a yanzu zai yi mummunan tasiri ga noman abinci, jaridar Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: An gano wani mutum mai mata 43 da yara sama da 200, ba a lissafa da yaransa mata ba

Ya ce:

"Mun yi matukar farin ciki cewa kalubalen 'yan fashi da satar mutane da suka addabi Zamfara, Katsina, Sokoto da ma Kaduna ba su shafi Kebbi ba.

“Birnin Kebbi tsibiri ne na zaman lafiya a cikin tekun yan fashi. Abinda ya faru kwanan nan abun damuwa ne. Yana nufin babbar haɗari ga tsaro a yankin arewa maso yamma.

“Kebbi ta zama cibiyar noman shinkafa a kasar nan. 'Yan Najeriya da yawa na cin shinkafa. Wannan wani dalili ne da ya sa wannan ci gaban ya tayar da hankali.”

Sai dai, ya bayyana cewa a Kaduna, gwamnatin jihar tana aiki tare da jami'an tsaro don magance matsalolin.

“A matsayin mu na gwamnatin jiha, akwai iyaka ga abin da za mu iya yi. Ba mu da cikakken iko a kan sojoji, ‘yan sanda ko sojojin sama.

“Hukumomin tsaro na ta yin iyakar kokarinsu. Dukanmu muna buƙatar kara zage damtse. Dole ne dukkanmu mu yi rawar gani a yanayin da muka samu kanmu," in ji shi.

Ya yaba wa gwamnatin tarayya kan goyon bayan da take bayarwa, sannan ya nuna kwarin gwiwa cewa nan ba da dadewa ba za a kawar da kalubalen tsaro a yankin.

Bayan Ganawa Da Buhari, Gwamna Bagudu Ya Bayyana Sunan Waɗanda Suka Sace Ɗaliban FGC Yauri

A gefe guda, Shugabannin Fulani na jihar Kebbi sun musanta zargin cewa suna da hannu a sace ɗaliban makarantar sakandiren gwamnatin tarayya FGC Yauri, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, shine ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da shugaba Buhari.

Gwamnan ya bayyana cewa shugabannin fulani a jihar Kebbi sun fito sun yi Allah wadai da satar ɗaliban, wanda wata ƙungiya da ake kira 'Renegade' suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel