Shugaba Buhari ya kai ziyara jihar Legas, zai kaddamar da wasu manyan ayyuka

Shugaba Buhari ya kai ziyara jihar Legas, zai kaddamar da wasu manyan ayyuka

- Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Legas domin kaddamar da ayyukan da gwamnatinsa ta yi a jihar

- Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban zai kaddamar da aikin layin dogo na farko da gwamnatinsa ta kammala

- Hakazalika rahoto ya ce zai zarce domin kaddamar da wani aikin a yankin Apapa dake birnin na Legas

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Legas domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatinsa ta cimma a yankin na Kudu maso Yammaci.

Sanarwa daga fadar shugaban kasa ta fitar a ranar Laraba kuma Legit.ng Hausa ta samo ta bayyana cewa, shugaban zai ziyarci jihar ta Legas ne a yau Alhamis 10 ga watan Yuni, 2021 domin kaddamar ayyukan, ciki har da na layin dogo mai tsawon kilomita 156.

KU KARANTA: Bankuna a Najeriya sun fara jan cajin USSD N6.98, masana sun bayyana illar haka

Shugaba Buhari ya kai ziyara jihar Legas, ya zarce kaddamar da wani katafaren aiki
Shugaba Buhari ya kai ziyara jihar Legas, ya zarce kaddamar da wani katafaren aiki Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Wani yankin sanarwar na cewa:

"Shugaba Muhammadu Buhari a gobe zai kaddamar da layin dogo mai tsawon kilomita 156 Legas zuwa Ibadan a jihar Legas, layin dogo na farko mai hawa biyu a Afirka ta Yamma, kuma layin dogo na farko na Najeriya da wannan gwamnatin ta fara kuma ta kammala, tun daga shekarar 1960."

Hakazalika, sanarwar ta ce an fara aikin ginin layin dogon ne tun shekarar 2017.

Rahotanni sun bayyana cewa, a yanzu haka shugaban yana Ebutte Meta Terminal na Kamfanin Jirgin Kasa na Najeriya don bikin kaddamar da aikin da kuma kafa tutar fara kasuwanci, in ji Channels Tv.

Bayan haka, ana sa ran zai wuce zuwa Energy Nature Light Terminal dake Apapa domin kaddamar da aikin Hadakar Tsaro ta Kasa da Kayayyakin Ruwa da aka fi sani da Deep Blue Project.

KU KARANTA: Da dumi: dumi: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure 3 a jihar Kaduna

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk nadin da yake yi ya dogara ne da cancanta ba wai kabilanci ko yanki ba.

Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ganawa da gidan talabijin na Arise TV. An soki shugaban kasar kan zargin nada wasu karin ‘yan arewa a manyan mukamai. A cikin hirar, shugaban na Najeriya ya ce ba zai iya sanya daidaito fiye da cancanta a nade-nadensa ba.

Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bayyana cewa ya kamata a raba manyan nade-nade yadda zai dauki bangarorin tarayya, wannan shine daidaito a tsakanin jihohi 36.

Asali: Legit.ng

Online view pixel