Shugaba Buhari ya bayyana yadda yake bi wajen nada mukaman gwamnati

Shugaba Buhari ya bayyana yadda yake bi wajen nada mukaman gwamnati

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana matakin da ya ke bi wajen nada mukarrabansa

- A cewarsa, cancanta yake bi ba wai bangaranci ko kabilanci ba don samun biyan bukata yadda ya dace

- Ya bayyana haka ne da yake amsa tambayar dalilin da yasa ya zabi shugaban hafsan soji Janar Faruk Yahaya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk nadin da yake yi ya dogara ne da cancanta ba wai kabilanci ko yanki ba.

Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ganawa da gidan talabijin na Arise TV.

An soki shugaban kasar kan zargin nada wasu karin ‘yan arewa a manyan mukamai. A cikin hirar, shugaban na Najeriya ya ce ba zai iya sanya daidaito fiye da cancanta a nade-nadensa ba.

KU KARANTA: Majalisa na zargin NIRSAL da yin sama da fadi da N105bn kudin manoma

Shugaba Buhari ya bayyana yadda yake bi wajen nada mukarrabansa
Shugaba Buhari ya bayyana yadda yake bi wajen nada mukarrabansa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Twitter

Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bayyana cewa ya kamata a raba manyan nade-nade yadda zai dauki bangarorin tarayya, wannan shine daidaito a tsakanin jihohi 36.

A cikin bayanin nasa kan batun nadin sabon shugaban hafsan soji, shugaban ya kuma ce ba zai iya fifita wadanda suka yi shekaru kadan a aiki ba kan wadanda suka dade.

“Mutanen da suka kasance a can na tsawon shekaru 18 ko ma na shekaru 10, sun yi horo a Zaria ko a Abeokuta, sun zo matsayinsu ta hanyar da ta dace.

“Saboda sun yi aiki a karkashin duk halin da ake ciki, rikice-rikice da komai kuma a hankali suka tashi zuwa wannan matsayin a haka kuke tunanin za ku zabi wani ne kawai don daidaitawa? Wadannan mukamai dole ne a bi cancanta” inji shi.

Nadin Shugaban Hafsun Sojojin na kasa, Yahaya Faruk, ya saba da ikirarin Shugaban kasar, in ji Premium Times.

An zabi Mista Yahaya ne sabanin manyansa wadanda suka shafe shekaru a aikin kuma yanzu za a tilasta musu yin ritaya.

KU KARANTA: Bankuna a Najeriya sun fara jan cajin USSD N6.98, masana sun bayyana illar hak

A wani labarin, Sakamakon rikice-rikicen rashin tsaro a kasar, kungiyar tuntuba ta kasa (NCFront), karkashin jagorancin Alhaji Ghali Umar Na'Abba da Farfesa Pat Utomi, sun roki tsoffin Shugabannin kasa da su “kwato Najeriya daga yakin basasa da ke tafe.”

A wata sanarwa da Karamin Ministan Tsaro (Navy), Dokta Olu Agunloye ya karanta a karshen taron da ta yi jiya a Abuja, kungiyar ta ce:

“Muna kira ga dattijan kasa da su dakatar da hutunsu na dan lokaci tare da daukar nauyin ceton Najeriya daga hallaka gaba daya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel