Afaka39: Hukumar Soji ta saki sunayen daliban da aka ceto daga hannun yan bindiga

Afaka39: Hukumar Soji ta saki sunayen daliban da aka ceto daga hannun yan bindiga

- An bayyana sunayen daliban da gwamnatin Kaduna tace an ceto daga hannun yan bindiga

- Daga cikin dalibai 39, an samu nasarar kubutar da guda biyar

- Gwamnan jihar Kaduna ya lashi takobin cewa ba zai biya yan bindiga kudin fansa ba

Hukumar Sojin Najeriya ta saki sunayen daliban makarantar FCFM Afaka, jihar Kaduna da aka ceto bayan garkuwa da su a harin da aka kai makarantar ranar 11 ga Maris, 2021.

A cewar Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Mohammed Yerima, an samu nasarar ceto biyar cikin dalibai 39 da aka sace.

Daliban Abubakar Yakubu, Francis Paul, Obadiya Habakkuk, Amina Yusuf da Maryam Danladi, a cewarsa.

"Daliban da aka ceto yanzu haka ana duba lafiyarsu a asibitin Sojoji dake Kaduna," yace.

"GOC na 1Div, Manjo Janar DH Ali-Keffi ya jinjinawa Sojojin bisa jajircewansu kuma ya yi kira da kada suyi kasa a gwiwa wajen ceto dukkan sauran daliban."

Zaku tuna cewa a ranar Litinin, gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da ceto dalibai 5 cikin wadanda aka sace a makarantar FCFM Afaka.

DUBA NAN: Zamu yafewa duk Fursunan da ya dawo kurakuransa, Gwamnati ga Fursunoni 2000 da suka gudu a Owerri

Afaka39: Hukumar Soji ta saki sunayen daliban da aka ceto daga hannun yan bindiga
Afaka39: Hukumar Soji ta saki sunayen daliban da aka ceto daga hannun yan bindiga
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya zabi Ahmed Garba matsayin Sabon sarkin Kagara

A bangare guda, mahaifin daya daga cikin daliban makarantar FCFM Afaka 39 da yan bindigan suka sace a jihar Kaduna, Ibrahim Shamaki, ya mutu.

Channels TV ta rahoto cewa Ibrahim, mahaifi ne ga Fatima Shamaki, daya daga cikin dalibai matan da suka bayyana a bidiyon da yan bindigan suka saki.

A cewar majiya daga iyalan mamacin, Ibrahim Shamaki ya mutu sakamakon bugun zuciya bayan rashin lafiyan da ya fada bayan samun labarin sace diyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel