Sojoji sun kubutar da dalibai 5 daga cikin 39 da 'yan bindiga suka sace a Kaduna

Sojoji sun kubutar da dalibai 5 daga cikin 39 da 'yan bindiga suka sace a Kaduna

- Sojoji sun samu nasarar kwato dalibai 5 cikin dalibai 39 na kwalejin noma dake jihar Kaduna da aka yi garkuwa dasu

- Kwamishinan tsaro na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata takarda da suka saki a ranar Litinin

- Dama tun ranar 12 ga watan Maris 'yan bindiga suka yi garkuwa da daliban makarantar dake karamar hukumar Igabi

Sojoji sun samu nasarar kubutar da dalibai 5 cikin 39 wadanda 'yan bindiga suka yi garkuwa dasu a FCFM dake Kaduna.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Litinin, The Cable ta ruwaito.

'Yan bindigan sun yi garkuwa da daliban a makarantarsu dake Afaka, karamar hukumar Igabi dake jihar Kaduna a ranar 12 ga watan Maris.

KU KARANTA: Zakakuran sojin Najeriya sun sheke 'yan ta'adda 7 da suka kaiwa tawagar Zulum hari

Sojoji sun kubutar da dalibai 5 daga cikin 39 da 'yan bindiga suka sace a Kaduna
Sojoji sun kubutar da dalibai 5 daga cikin 39 da 'yan bindiga suka sace a Kaduna. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

A cewar Aruwan, yanzu haka sojoji sun dauki dalibai 5 zuwa asibiti don tabbatar da ingancin lafiyarsu.

Kamar yadda takardar tazo, "Sojojin Najeriya sun bayyana wa gwamnatin jihar Kaduna cewa sun kubutar da 5 daga cikin daliban FCFM, Afaka da aka yi garkuwa dasu da ranar nan, kuma yanzu haka suna asibiti ana kulawa da lafiyarsu.

"Gwamnatin jihar Kaduna zata cigaba da bayar da bayanai idan wani abu ya sake faruwa."

Duk da takardar bata kara bayani akan yadda al'amarin ya faru ba, iyayen daliban sun lashi takobin sasantawa da masu garkuwa da mutane don tabbatar da sakin yaransu.

A makonni 2 da suka gabata, sai da iyayen daliban suka yi zanga-zanga akan aukuwar lamarin, suna cewa sun yi iyakar kokarinsu don tabbatar da an saki yaransu.

KU KARANTA: Mun shirya yin sasanci da ƴan bindigan da suka sace ƴaƴanmu, Iyayen ɗaliɓan Kaduna

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta bataliya ta 192 dake karamar hukumar Gwoza a jihar Borno sun samu nasarar kashe a kalla wasu 'yan ta'adda 12 da ake zargin 'yan Boko Haram ne, jaridar The Cable ta ruwaito.

Da tsakar daren Lahadi ne 'yan ta'addan suka kaiwa sansanin sojojin farmaki. Majiyoyi da dama sun sanar da The Cable cewa sojojin sun yi musayar wuta dasu.

"Rundunar Tango 9 sun yi gaggawar mayar da harin da 'yan ta'adda suka kai musu har suka kashe mutane 7 take yanke, hakan yasa suka ja da baya," Kamar yadda majiyar ta tabbatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel