Zamu yafewa duk Fursunan da ya dawo kurakuransa, Gwamnati ga Fursunoni 2000 da suka gudu a Owerri

Zamu yafewa duk Fursunan da ya dawo kurakuransa, Gwamnati ga Fursunoni 2000 da suka gudu a Owerri

- Ministan Buhari ya yi kira ga wadanda suka gudu daga gidan gyaran hali su dawo cikin ruwan sanyi

- Ministan ya musu alkawarin yafe musu muddin har suka dawo da kansu

- Akalla mutum shida sun dawo kawo yanzu cikin wadanda suka arce ranar Talata

Ministan harkokin cikin gida, Rauf AregbeSola ya yi kira ga Fursunonin da suka gudu daga gidan yarin Owerri cewa su dawo da kansu.

Ministan ya yi alkawarin cewa duk Fursunan da ya dawo, za'a yafe masa kura-kuransa.

Aregbesola ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara ta musamman gidan yarin a ranar Talata biyo bayan harin da yan ta'addan IPOB suka kai.

Ya ce guduwa daga gidan yari laifi ne amma yana bada tabbacin cewa duk wanda ya dawo ba za'a hukuntashi ba.

DUBA NAN: Dukiyar Aliko Dangote, Mike Adenuga da Abdussamad Rabiu ta karu da Naira Tiriliyan 2 a 2021

Zamu yafewa duk Fursunan da ya dawo kurakuransa, Gwamnati ga Fursunoni 2000 da suka gudu a Owerri
Zamu yafewa duk Fursunan da ya dawo kurakuransa, Gwamnati ga Fursunoni 2000 da suka gudu a Owerri Credit: @raufaregbesola
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kasar Indiya ta baiwa Najeriya gudunmuwar rigakafin Korona guda 100,000

Hakazalika Ministan ya lashi takobin cewa wadanda suka kai hari gidan yarin zasu fuskanci fushin hukuma.

Yace: "Guduwa daga gidan yari laifi ne amma gwamnati za ta bada afuwa ga Fursunonin da suka dawo da kansu."

"Ba za'a kamasu da laifin yunkurin guduwa ba amma zasu cigaba da zama kan laifukan da suka aikata a baya. Saboda haka muna kira da su dawo kafin a kama su."

Mataimakin kwantorolan gidan yarin, Seye Oduntan, ya bayyana cewa fursunoni 36 sun ki guduwa yayinda guda 6 suka dawo da kansu.

A bangare guda, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bada umarni ga jami'ai da kada su tausayawa masu rajin kafa kasar Biafra (IPOB).

Sifeta janar na 'yan sandan ya bada wannan umarnin ne yayin da ya ziyarci hedkwatar hukumar 'yan sandan Imo da aka kona da kuma gidan gyaran hali na Owerri a ranar Talata.

Adamu ya sanar da cewa dole ne 'yan sanda su yi amfani da makamansu wurin mitsike duk wani mai tada kayar baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel